logo

HAUSA

Kasar Sin ta fitar da ka’idoji kan lura da fitar da kayayyaki masu amfani biyu

2024-10-19 20:16:22 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Qiang ya rattaba hannu da kuma kaddamar da ka’idojin kasar Sin kan lura da fitar da kayayyaki masu amfani biyu, wadanda za su fara aiki daga ranar 1 ga watan Disamba na shekarar 2024.

La’akari da kiyaye tsaron kasa baki daya, an tsara ka’idojin wadanda suka kunshi babi shida da bayanai 50 ne, don wanzar da zaman lafiyar kasa da kasa, da daidaita ci gaba mai inganci tare da tsaro a babban mataki, da inganta karfin lura da fitar da kayayyaki masu amfani biyu.

Kayayyaki masu amfani biyu suna nufin hajoji da fasaha da kuma hidimomi wadanda ake amfani da su ko dai don dalilai na jama'a ko don dalilai na soja ko kuma don ba da gudummawa ga habaka karfin soja, musamman don tsara fasali, ko habaka, samarwa ko amfani da makaman kare dangi da hanyoyin isar da su. (Yahaya)