Bankin raya kasashen Afrika zai samar da bankin saka jari a bangaren sana'o'in dogaro da kai ga matasa a Najeriya
2024-10-19 15:20:52 CMG Hausa
Bankin raya kasashen Afrika ya sha alwashin samar da bankin da zai mayar da hankali wajen zuba jari ga harkokin sana'o'in dogaro da kai ga matasa a tarayyar Najeriya.
Shugaban bankin Mr. Akinwunmi Adesina ne ya tabbatar da hakan jiya Juma`a 18 ga wata a birnin Abuja yayin jawabin da ya gabatar wajen taron lacca a kan cika shekaru 90 da haihuwar tsohon shugaban Najeriya Janaral Yakubu Gowon.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Mr Akinwunmi Adesina ya bayyana cewa a kwanaki ukun da suka gabata hukumar daraktocin bankin na AFDB ya amince da samar da tsabar kudi har dala miliyan 100 wajen assasa bankin zuba jarin kan sana'o'in hannu a tarayyar Najeriya.
Shugaban ya ce babu shakka yunkurin samar da bankin ya biyo bayan amincewar da bankin na raya kasashen Afrika ya yi ne nacewa matasa su ne ginshikin cigaban kasa.
Mr Adesina ya yi bayanin cewa sabon bankin idan aka samar da shi zai taimakawa harkokin kasuwancin matasa a Najeriya ta hanyar bayar da horon fasaha, da ilimin koyon dabarun kirkirar sana'o'i da saka jari, inda ya yi fatan cewa wannan mataki zai kawo karshen yawaitar kaurar al`umma.
Kamar yadda shugaban bankin raya kasashen Afrikan ya fada, adadin matasan da suke kaura da kafafun babban barazana ne ga ci gaban kasa.
Koda yake ya danganta hakan ga matsin rayuwa da ake fama da shi, amma dai ya ce duk da hakan za a iya samun daidaituwar al'umura idan an koma ka'in da na'in bisa tsarin sana'o'in da suke da nasaba da fasahar zamani. (Garba Abdullahi Bagwai)