Karuwar Tattalin Arzikin Sin Na Sa Kaimi Ga Kamfanonin Duniya Da Su Hada Kansu Da Sin
2024-10-19 17:08:18 CMG Hausa
Alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta bayar sun nuna cewa, yawan GDPn kasar Sin daga watan Janairu zuwa Satumban bana, ya karu da 4.8% kan na makamancin lokacin bara.
Lalle kasar Sin ba ta samu wannan karuwa cikin sauki ba. Tun daga farkon bana, an gamu da matsaloli da dama ta fuskar raya tattalin arziki a kasashen duniya, kasar Sin ta kuma sha wahala bisa kwaskwarimar da ta yi kan harkokin tattalin arziki. Amma kasar Sin ta cimma nasarar warware matsalolin dake gabanta, kana nagartattun manufofi da dama da ta fita, sun tabbatar da karuwar tattalin arziki cikin yanayi mai karko.
Kwanan baya, kamfanin Apple na kasar Amurka ya kafa dakin gwaje-gwaje da nazari a birnin Shenzhen na kasar Sin, a watan Satumba kuma, kamfanin Audi na kasar Jamus ya sanar da kafa sabon tsarin raya kasuwanni a kasar Sin, kana, kamfanin aikin jinya na GE na kasar Amurka ya ce, jarin da zai zuba a kasuwannin kasar Sin zai ninka sau biyu cikin shekaru 3 masu zuwa. Dalilin da ya sa kamfanonin suka dauki wadannan matakai, shi ne, domin ba kawai suna son shiga cikin kasuwannin kasar Sin ba, har ma suna fatan hada kansu yadda ya kamata da kasuwannin kasar Sin, ma’anar ita ce, suna fatan habaka kasuwannin kasar Sin zuwa kasuwannin kasashen duniya, ta hanyar zurfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu da kasar Sin.
Karuwar tattalin arzikin Sin cikin watanni 9 da suka gabata, ya ba da tabbaci ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar bana, tare da manufofin da gwamnatin kasar ta fidda, tabbas, za a samar da karin damammaki ga bunkasuwar tattalin arziki cikin yanayi mai kyau. Kasar Sin tana da imanin cimma burinta na samun karuwar GDPn da 5% a bana. A sa’i daya kuma, kasashen duniya da kasar Sin za su cimma moriyar juna, tare da samu ci gaba tare. (Mai Fassara: Maryam Yang)