logo

HAUSA

Nijeriya ta gabatar da sabon allurar riga kafin cutar zazzabin cizon sauro

2024-10-18 14:20:31 CMG Hausa

Nijeriya ta gabatar da sabon rigakafin cutar zazzabin cizon sauro na malaria da za a bayar kyauta a kasar, wanda wani muhimmin mataki ne a yaki da cutar da ta yi sanadin mutuwar dubban yara ’yan kasa da shekaru 5 a kasar mafi yawan jama’a a Afrika.

Ministan lafiya na Nijeriya Ali Pate, ya ce kasar ta sayi rigakafi 846,200 bisa hadin gwiwa da hukumar GAVI, ta kawancen kasashen duniya kan samar da rigakafi da kuma asusun kula da kananan yara na MDD (UNICEF).

Ministan ya kara da cewa, kafin karshen wannan wata, ana sa ran isar da wasu alluran guda 153,800 a kasar, inda jimilarsu za ta kai miliyan 1. (Fa’iza Mustapha)