Yawan karuwar GDPn Sin daga watan Janairu zuwa Satumban bana ya kai 4.8% bisa na makamancin lokacin a bara
2024-10-18 11:27:52 CMG Hausa
Yau Juma’a da safe, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar Sin ya kira taron manema labarai, inda ya yi bayyani kan yanayin tafiyar tattalin arzikin al’umma daga watan Janairu zuwa Satumban bana. Alkaluman da hukumar kididdiga ta bayar na nuna cewa, yawan GDPn kasar Sin daga watan Janairu zuwa Satumban bana, ya kai fiye da dala triliyan 13, abin da ya karu da kashi 4.8% kan na makamancin lokacin a bara, bisa darajar kudi wancan lokaci.
Ban da wannan kuma, a wannan lokaci, yawan karuwar darajar masana’antu ya kai kashi 5.8% bisa na makamancin lokaci a bara, wanda shi ne muhimmin ma’aunin bunkasuwar tattalin arzikin kasa. (Amina Xu)