logo

HAUSA

Gudunmawar Da Sin Take Bayarwa Wajen Tabbatar Da Wadatar Abinci A Duniya

2024-10-18 17:00:48 CMG Hausa

DAGA MINA

Ranar 16 ga watan nan da muke ciki, rana ce ta tabbatar da wadatar abinci a duniya. Sai dai ta yaya za a iya tabbatar da wannan batu, da ya zama abin da gwamnatocin kasa da kasa suke mai da hankali kansa a ko da yaushe? Bari mu tantance kokarin da Sin ta yi a wannan bangare, da gudunmawar da take bayarwa duniya.

A shekarar 1949, lokacin da aka kafa jamhuriyar jama’ar kasar Sin, yawan hatsin da Sin ta samu shekara daya bai wuce ton miliyan 113.2 ba. Amma a shekarar 2023, wannan adadin ya kai ton miliyan 695, kuma an tabbatar da samun yawan hatsin da ya kai kimanin ton miliyan 650 a cikin shekaru 9 a jere, lamarin da ya sanya Sin samun yabanya mai yalwa cikin shekaru 20 a jere. Kana matsakacin yawan hatsin da kowane Basine ya samu a duk shekara ya kai kilo 493, adadin da ya zarce kilo 400, wanda ya zama ma’aunin duniya na samun wadatar abinci ga ko wane mutum. Abun da ya bayyana cewa, Sinawa na samun wadatar abinci bisa jagorantar da gwamnatinsu ta yi, gami da kokarinsu.

Mene ne dalilin da ya sa aka samu wannan nasara? Shi ne domin tsarin kare gonaki na kasar, da yadda take yayata fasahar aikin gona. Ya zuwa karshen shekarar 2023, yawan ingantattun gonakin da Sin ta mallaka ya kai fiye da muraba’in kilomita dubu 667. Kuma ba tabbatar da yawansu kadai kasar Sin take yi ba, tana dukufa kan tabbatar da ingancinsu. Kazalika, yawan gudunmawa ta fuskar kimiyya da fasaha da aka samar a bangaren aikin gona a shekarar 2023 ya kai kashi 63.2%, adadin da ya karu da kashi 8.7% bisa na shekarar 2012, matakin da ya sa Sin zama daya daga cikin kasashe mafiya karfin kimiyya da fasahar aikin gona. Sabbin nau’o’in kimiyya da fasaha da Sin take bayarwa, na taimakon kokarin tabbatar da wadatar abinci.

Ban da wannan kuma, hanyar da Sin take bi na tabbatar da wadatar abinci, ya zama abun koyi ga kasashe daban daban, kuma Sin tana hadin gwiwa da sauran kasashe wajen yada fasahohinta. Alali misali, kasar Madagascar, ta rungumi fasahar noman shinkafar da aka tagwaita ta Sin, inda yawan shinkafar da ake nomanta a Madagascar ya kai kadada dubu 70, kana yawan hatsin da ake girba kan kadada daya ya kai ton 7, wani lokaci har ya kan kai ton 12, adadin da ya ninka har sau 2 bisa na nau’in shinkafar asali da ake nomansu a kasar. Ta la’akari da bukatun da ke akwai a kasar Madagascar a duk shekara, za a samu damar tabbatar da wadatar abinci a kasar, idan aka kara shuka irin shinkafar Sin a gonaki masu fadin kadada dubu 100. Domin tunawa da taimakon da Sin ta ba kasar a bangaren shuka shinkafar da aka tagwaita, Madagascar ta buga hoton shinkafar Sin a kan takardar kudinta.

Sin ta taka rawar gani wajen tabbatar da wadatar abinci. Kuma tana kokarin gabatar da dabarunta ga sauran kasashe. Shi ya sa, karin kasashe masu tasowa, ciki har da kasashen Afrika, ke da damar tabbatar da wadatar abinci, ta hanyar amfani da fasahar Sin. Sinawa su kan ce “More tare da sauran mutane ya fi jin dadin wani abu mutum daya kadai ”. Sin na son raba dabararta ta hanyar hadin gwiwa da sauran kasashe a dukkan fannoni. (MINA)