logo

HAUSA

Gwamnatin Najeriya: mafi yawan makaman da ’yan bindiga ke amfani da su mallakin gwamnati ne

2024-10-18 09:22:40 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana takaicin yadda ’yan bindiga ke amfani da makamai mallakin gwamnati wajen gudanar da ayyukan ta’addancin a kasar.

Mashawarcin shugaban kasa a kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu ne ya bayyana hakan jiya Alhamis 17 ga wata a birnin Abuja yayin bikin lalata manya da kananan makamai da cibiyar shawo kan yaduwar makamai ta kasa ta gudanar.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Malam Nuhu Ribadu ya yi alawadai da halayyar wasu baragurbin ma’aikatan hukumomin tsaron kasar inda ake hada baki da su wajen samar da makamai ga ’yan ta’adda. Ya jaddada cewa, babu shakka irin wannan halayya illa ce babba ga yanayin tsaron kasa.

A cikin jawabin nasa, mashawarcin shugaban kan harkokin tsaro ya sanar da cewa, a iya binciken da gwamnati ta yi ta gano cewa, da yawa daga cikin nau’ikan makaman da ’yan bindiga suke amfani da su a kasar suna samun su ne daga rumbunan ajiyar makamai na gwamnati, a don haka Malam Nuhu Ribado ya yi kiran da a dauki kwararan matakai da za su kara dakatar da wannan mummunar halayya muddin dai ana bukatar samar da dauwamammen zaman lafiya a kasa.

Malam Nuhu Ribado ya ce, zai yi wahala a iya misalta muhimmancin shirin lalata makaman, wanda yana daya daga cikin kokarin da ake yi na dakile yaduwar makamai a kasar da ma kasashen dake yammacin Afrika baki daya.

Sama da makamai 2,400 ne aka samu damar lalatawa yayin bikin wadanda suka kunshi manya da kananan bindigu, kuma bikin ya samu halartar darakta janaral na cibiyar da babban hafsan tsaron Najeriya Janaral Christopher Musa da kuma sauran wakilan hukumomin tsaron kasar.  (Garba Abdullahi Bagwai)