logo

HAUSA

Ofishin jakadancin Italiya da ke Nijar na bikin cikon shekara 40 na shirin aiki na « Projet Keita »

2024-10-18 09:26:12 CMG Hausa

A jamhuriyyar Nijar, a ranar jiya Alhamis 17 ga watan Oktoban shekarar 2024, ofishin jakadancin kasar Italiya dake Yamai ya yi bikin tunawa da cikon shekaru 40 da shirin aiki na Keita, dake matsayin wani sakamako na kyaukyawar dangantakar dake tsaknin kasashe biyu.

Daga birnin Yamai, abokin aaikinmu ya aiko mana da wannan rahoto. 

Shi dai wannan babban shirin aiki na Keita ko “Projet Keita”, duk da cewa shekaru sun wuce sosai, har yanzu yana cikin zukatan ’yan Nijar. Makasudin wannan aiki shi ne na farfado da muhallin halittu wato kasa, ruwa, da noma a yankin Tahoua.

Bikin cikon shekaru 40 na shirin aiki na “Projet Keita” na bayyana ci gaba mai kyau tsakanin kasashen biyu.

Dangantaka tsakanin Italiya da Nijar na bisa turba mai kyau har yanzu, in ji mai kula da harkoki na ofishin jakadancin Italiya dake Nijar, mista Reberto Orlando, da kuma take shafar muhimman fannoni da suka hada da tsaron abinci, yaki da bakuncin haure, ilimi, horo zuwa makarantun koyar da aikin hannu, da cin gashin kai mata, mulki na-gari, gine-gine da kuma yaki da hamada.

Bikin kaddamarwa na cikon shekaru 40 na shirin “Projet Keita” ya gudana a karkashin jagorancin wakilin ministan harkokin waje, Omar Sidi Ibrahim, tare da halartar gwamnan birnin Yamai da sauran baki.

Shirin ci gaban karkara na Ader-Doutchi-Magaria- PDR-ADM da ake kira shirin aiki na Keita ko “Projet Keita” an yi shi tsakanin shekarar 1984-2001 tare da kudin tallafin kasar Italiya na dalar Amurka miliyan 784.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.