logo

HAUSA

Sin na kara haskakawa a fagen wasan tennis

2024-10-17 20:59:58 CMG Hausa

A gabar da aka kammala gasannin kwallon tennis na kasar Sin da suka hada da “China Open”, da “WTA 1000 Wuhan Open”, da “ATP 1000 Shanghai Masters”, ana iya cewa kakar wasan ta kasar Sin ta gabanin shigar lokacin hunturu tana dada jan hankalin masoya tennis na dukkanin sassan duniya.

Kamar dai yadda aka wallafa a shafin yanar gizo na ATP, kasar Sin ta karbi bakuncin jerin gasannin tennis tun daga watan Satumba, ciki har da na “Chengdu Open”, da “Hangzhou Open”, da “China Open”, da “Shanghai Masters”. Kaza lika, mahukuntan gasar WTA sun wallafa a shafin yanar gizo, cewa jerin gasanni kamar “Guangzhou Open”, da “Jiangxi Open”, da “Ningbo Open”, da “Wuhan Open” na cikin gasannin da suka dauki hankali sosai.

Cikin wannan jeri, gasannin “Chengdu”, da na “Hangzhou Opens”, na cikin rukunin ATP 250, yayin da na “Guangzhou”, da “Jiangxi Opens” ke cikin rukunin gasannin WTA 250. Sai kuma “Shanghai Masters” wadda ke matsayin “ATP 1000”. Kaza lika, akwai “Wuhan Open”, da “China Open” dake cikin rukunin gasannin “WTA 1000”.

Karin gudanar gasannin kasa da kasa na wasan tennis a kasar Sin na da nasaba ne da yadda masoya wasan ke kara nuna sha’awar su gare shi bayan gudanar da babbar gasar “Grand Slam”, wadda ta share fagen zuwan tarin gasannin "Kakar wasannin kasar Sin".

Kakar wasannin kasar Sin tana da dogon tarihi, kuma manufarta shi ne jerin wasannin tenis na ajin kwararru da ake bugawa a kasar Sin a lokacin bazara, da kafin shiga lokacin hunturu. An bude gasannin ATP 250 na biranen Hangzhou, da Chengdu ne tun daga ranar 18 ga watan Satumba, kamar dai yadda mataimakin sakataren hukumar lura da wasan tennis na kasar Sin Lyu Liang ya tabbatar.

A cewar Lyu, "Manyan gasannin tennis na dunkule da juna a matakin kasa da kasa, suna bin tsari iri daya da ba a ga irin sa ba kafin zuwan manyan gasannin “Grand Slam”. Ya ce kakar bana na da fa’ida ga manyan ‘yan wasa, inda take ingiza tallata wasan, da fadada darajar cinikayyarsa, da bunkasa tattalin arzikin wuraren da ake gudanar da ita.

A nasa bangare kuwa, mataimakin shugaba, kuma babban sakataren hukumar gudanar da gasar tennis ta kasar Sin Bai Xilin, ya ce “Kakar wasan tennis ta Sin” na da muhimmanci wajen bunkasa wasan. Kaza lika, manyan gasanni na da tasiri wajen horas da manyan ‘yan wasa, suna kuma baiwa sabbin ‘yan wasan Sin matasa damar fafatawa da manyan ‘yan wasa na kasa da kasa, tare da kara samun gogewa.

Yayin da taurarin ‘yan wasa matasa irin su Zheng Qinwen ke tasowa a matakin kasa da kasa, a yanzu kasar Sin ce kasa ta biyu a duniya a fannin yawan ‘yan wasan tennis, da yawan masu sha’awar wasan a duniya baki daya. Fadadar kasuwar wasan ta sanya hukumomin ATP da WTA, dora karin muhimmanci ga gasannin kasar Sin, wanda hakan ya yi matukar kara yawa da ingancin gasar.

Game da gasannin ATP, mataimakin shugaban ta na kasa da kasa Alison Lee, ya ce ana shirya gasannin rukunin ATP 4 a wurare mafiya dacewa dake kasar Sin. Ya ce “Bana shekara ce mai kayatarwa, wadda ta hallara dukkanin ‘yan wasan kasar Sin a gasar ta ATP. Kuma dukkanin gasannin na ATP sun samu masu daukar nauyin su sosai, a wasu lokutan ma, ana sayar da tikitin shigar su baki daya. A bara, sun ga karuwar masu kallo, bayan gaza kallon manyan wasannin kasa da kasa ido da ido, sakamakon annobar COVID-19. A bana muna hasashen karin masu kallo".

Sakamakon kara kyautatuwar wurare da kayan wasan, biranen kasar Sin na fatan karbar bakuncin manyan gasannin tennis, don kara inganta kimar su a matakin kasa da kasa, yayin da suke ingiza ci gaban tattalin arzikin su. Alkaluma sun nuna cewa, manyan wasannin shekarar 2024 sun samu matukar karbuwa, inda aka sayar da dukkanin tikitin kallon su tun a ranar 1 ga watan Oktoba, kuma ‘yan kallo 44,000 suka kalli wasa a rana daya kacal. Ana kuma hasashe jimillar masu kallon wasannin za su kai 300,000, karin kaso 50 bisa dari kan na shekarar bara. Yayin da kuma kudaden shiga masu nasaba da hakan za su kai kudin Sin yuan miliyan 80, adadin da zai karu da kaso 60 bisa dari kan na bara.

A cewar jami’an hukumar lura da harkokin wasanni na birnin Hangzhou, ingiza wasanni masu inganci na taimakawa, wajen daidaita tafiya tsakanin wasanni, da al’adu da yawon bude ido, tare da ingiza bunkasar tattalin arziki, da bude sabbin kofofi na damammaki.

Sakamakon wani bincike ya nuna cewa, wuce hasashen samun kudin shigar ‘yan kasar Sin na dala 8,000, zai fadada dukkanin fannonin wasannin kasar. Yayin da wasan kwallon tennis, ya game sassa daban daban da suka hada da samar da wuraren wasan, da kayan aiki, da horo, da gasanni, wadanda ke kara samun karbuwa a kasar Sin.

Idan an hangi gaba, ana iya hasashen yadda ‘yan wasan kasar Sin za su ci gaba da samun manyan nasarori a gasannin kasa da kasa, yayin da kwallon tennis ke cikin wasannin da za su yi babban tasiri a kasar, kuma kakar wasan ta kasar Sin, za ta ci gaba da zama wadda za a kara mayar da hankali a kan ta a duniyar wasan tennis.