logo

HAUSA

Sin ta yi kira a kare kwarjinin kudurin kwamitin sulhu na MDD

2024-10-17 13:24:40 CMG Hausa

Kwamitin sulhu na MDD ya kira taro cikin gaggawa game da yanayin da zirin Gaza ke ciki bisa bukatar kasar Aljeriya, a jiya Laraba 16 ga wata. Yayin taron, zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Fu Cong ya bayyana cewa, kwamitin sulhun ya riga ya zartas da wasu kudurori kan yanayin Gaza, wadanda suka bukaci a tsagaita bude wuta a yankin, amma ba a tabbatar da ko daya daga cikinsu ba, lamarin da ya gurgunta amanar tsarin majalisar ainun.

Fu Cong ya kara da cewa, wajibi ne a kare da kuma sake farfado da kwarjinin dokokin jin kai na kasa da kasa. Kuma dole ne dukkanin kasashen duniya su aiwatar da kudurin kwamitin sulhu na majalisar. Kana kasar Sin tana fatan Amurka za ta amsa kiran al’ummomin kasashen duniya kuma ta goyi bayan kwamitin sulhun da ya dauki matakan da suka dace domin cimma burin tsaigaita bude wuta a zirin Gaza nan take ba tare da bata lokaci ba.

Bugu da kari, jami’in ya yi nuni da cewa, ya dace kasashen duniya su dauki matakin da ya wajaba domin aiwatar da shirin “kafa kasashe biyu”. Yana cewa, kasar Sin tana son ci gaba da ba da gudummowarta domin tabbatar da zaman lafiya a yankin cikin sauri. (Jamila)