logo

HAUSA

Peng Liyuan ta taya murnar gudanar da bikin bayar da lambobin yabo kan bunkasa ilimin mata da ‘yan mata na UNESCO

2024-10-17 10:10:15 CMG Hausa

 

Peng Liyuan, uwargidan shugaban kasar Sin Xi Jinping, kuma jakadiyar musamman ta hukumar bunkasa ilimi, kimiyya da raya al’adu ta MDD (UNESCO) domin daukaka ilimin mata da ’yan mata, ta aike da sakon taya murna ga bikin bayar da lambobin yabo ga wadanda suka bunkasa harkokin da suka shafi ilimin mata da ’yan mata, wanda ya gudana jiya Laraba a birnin Paris na Faransa.

Cikin sakonta, Peng ta jinjinawa hukumomin da suka lashe lambobin yabon daga kasashen Uganda da Zambia, tare da yi musu fatan alheri.

Ta ce har kullum, kasar Sin ta kasance mai bayar da matukar muhimmanci ga harkokin da suka shafi ilimin mata da ’yan mata da ingiza burin duniya kan ilimin mata da ci gaba da inganta muhallin neman ilimi ga mata a kasar.

Peng Liyuan ta kara da cewa, a matsayinta na jakadiyar UNESCO kan daukaka ilimin mata da ’yan mata, a shirye take ta hada hannu da duk wani bangare domin hada karfi da karfe da nufin cimma daidaiton jinsi da burin duniya kan harkokin da suka shafi mata. (Fa’iza Mustapha)