logo

HAUSA

Mambobin kungiyar SCO sun bayyana adawa da matakan kariyar cinikayya

2024-10-17 10:28:11 CMG Hausa

Kasashe mambobin kungiyar hadin kai ta Shanghai (SCO), sun bayyana adawa da matakan kariyar cinikayya da takunkumai daga bangare guda da takaita harkokin cinikayya, wadanda ke illata tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban-daban da tarnaki ga samun ci gaba mai dorewa a duniya.

Cikin wata sanarwar hadin gwiwa da aka fitar bayan taron shugabannin gwamnatocin kasashe mambobin kungiyar karo na 23, shugabannin tawagogi sun nanata muhimmancin amfani da damarmakin dake akwai a kasashen yankin da hukumomin kasa da kasa da manufofin kasa da kasa, wajen gina wani budadden tsarin hadin gwiwa mai fadi bisa daidaito da moriyar juna, karkashin dokokin kasa da kasa da la’akari da muradun kasashe.

A yau Alhamis ne kuma firaministan Sin Li Qiang, ya dawo Beijing bayan halartar taron na 23 na shugabannin gwamnatocin kasashe mambobin kungiyar ta SCO a Pakistan da kuma ziyarar aiki a kasar. (Fa’iza Mustapha)