Kusan mutane miliyan 3 sun tsere daga Sudan sanadiyyar yakin da ya shafe watanni 18 a kasar
2024-10-17 10:34:23 CMG Hausa
Kusan mutane miliyan 3 da suka hada da ’yan gudun hijira da wadanda suka koma gida ne suka tserewa Sudan bayan yakin kasar da ya shafe watanni 18, inda suka tsallake iyaka zuwa kasashe makwabta da ma wasu kasashen dake nesa, domin samun mafaka. Galibi sun tsere ne zuwa kasashen Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya da Chadi da Masar da Habasha da Libya da Sudan ta Kudu da Uganda.
Ofishin kula da harkokin jin kai na MDD (OCHA), ya bayyana a jiya Laraba cewa, ya damu ainun da yadda rikici ke ci gaba da raba mutane da muhallansu a sassa da dama na Sudan.
Baya ga haka, ofishin ya ce MDD da abokan huldarta, na hada hannu da hukumomin lafiya na Sudan, domin bunkasa aikin tunkarar cutar amai da gudawa, ciki har da fadada bayar da riga kafi da wayar da kan jama’a da samar da ruwa mai tsafta da tsaftar jiki da muhalli. (Fa’iza Mustapha)