logo

HAUSA

Shugaba Bola Tinubu ya tura wata tawaga mai karfi zuwa jihar Jigawa bayan gobarar tankar man fetur da ya afku

2024-10-17 09:44:58 CMG Hausa

 

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya aike da wata tagawa zuwa jihar Jigawa domin kimanta adadin asarar da aka yiwa sakamakon hatsarin tankar man fetur da ya yi sanadiyar mutuwar sama da mutane 140 a garin Majiya.

Sakataren gwamnatin tarayya Mr Geoge Akume ne zai jagoranci tawagar da ta kunshi ministan tsaron kasar  Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar da na sufuri Sanata Sa’idu Alkali.

Bugu da kari, shugaban majalissar karamar hukumar Taura dake jihar Jigawa Alhaji Shu’aibu Hambali ya tabbatar da a yammacin jiya Laraba cewa, adadin yawan mutanen da aka tabbatar sun rasa rayukansu sakamakon hatsarin tankar man fetur da ya faru a daren Talata a jihar Jigawa ya kai 147 a tsididdgar da aka gudanar jiya Laraba 16 ga wata, sabanin mutane 105 da aka sanar tun da farko.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Daga cikin wuraren da tawagar za su ziyarta sun hada da wurin da hatsarin ya faru domin dai su kimanta adadin barnar da gobarar ta yi, sannan kuma za su gana da mutanen da suka sami raunuka wadanda kuma suke kwance a asibitin dake yankin.

Bayan da ya sami rahoton afkuwar hatsarin gobarar, shugaban na tarayyar Najeriya ya bayar da umarnin kai daukin gaggawa da suka kunshi samar da magunguna da kayan abinci da matsugunai na wucin gadi ga mutane 50 da hatsarin ya shafa wanda kuma yanzu haka ake ci gaba da lura da lafiyarsu. 

Bayan ya bayyana damuwa da jajensa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu, shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sha alwashin cewa, gwamnatin tarayya za ta hada hannu da jihohi wajen sake duba tsarin dakon man fetur ta amfani da motoci a duk fadin kasar, sannan kuma ya umarci hukumar kiyaye afkuwar hadura ta kasar da ta kara matsawa sosai ta hanyar sanya ido domin dai tabbatar da ganin ana kiyayewa da dokokin tuki musamman ga direbobin masu tafiyar dare. (Garba Abdullahi Bagwai)