logo

HAUSA

Firaministan Sin ya halarci ganawa da takwarorinsa na Rasha da Mongolia

2024-10-16 16:10:32 CMG Hausa

A yau Laraba 16 ga wata, yayin da ake ci gaba da gudanar da taro na 23 na majalissar faraministocin kasashe mambobin kungiyar hadin kai ta Shanghai a birnin Islamabad na Pakistan, firaministan kasar Sin Li Qiang, ya gana da takwarorinsa na Rasha Mikhail Vladimirovich Mishustin, da na Mongolia Luvsannamsrai Oyun Erdene.

Yayin zaman na su, Li Qiang ya bayyana aniyar kasar Sin ta zurfafa hadin gwiwar sassa daban daban tare da Rasha da Mongolia, bisa matsaya daya da shugabannin kasashen 3 suka amince, da aiki tare don ci gaba da bude sabon babin hadin gwiwar kasashen 3 a sabon zamani.

A nasu bangare kuwa, mista Mishuskin, da Oyun Erden, cewa suka yi Rasha da Mongolia a shirye suke su yi aiki tare da Sin, wajen karfafa dunkulewar tattalin arzikin yankin Turai da Asiya, da hada hannu wajen gina shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya", da gaggauta gina zirin tattalin arziki na Sin, da Mongolia da Rasha, da ingiza hadin gwiwar sassan 3 don cimma karin nasarori.

Yayin taron, Li Qiang ya kuma zanta bi da bi, da firaministocin kasashen Tajikistan da Rasha.  (Saminu Alhassan)