logo

HAUSA

Li Qiang ya halarci taron majalisar shugabannin gwamnatocin kasashe mambobin SCO karo na 23

2024-10-16 19:55:07 CMG Hausa

A yau ne, firaministan kasar Sin Li Qiang ya halarci taron majalisar shugabannin gwamnatocin kasashe membobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai ko SCO karo na 23 a birnin Islamabad.

A yayin taron, Li Qiang ya gabatar da shawarwari hudu kan yadda za a zurfafa hadin gwiwar kasashe membobin kungiyar, na farko dai, a kara yin mu’amala da juna bisa ayyukan da aka cimma daidaito, wato a tsara manufofin bunkasa kungiyar SCO na shekaru 10 masu zuwa da kuma taswirar hadin gwiwar kasashe membobin kungiyar a dukkan fannoni, da kara yin mu’amala da juna da warware matsaloli ta hanyar yin shawarwari da kuma kara amincewa da juna. Na biyu, a fadada hadin gwiwa bisa bukatun samun ci gaba, wato a zurfafa hadin gwiwar kasashe membobin kungiyar a fannonin yaki da talauci, da tattalin arziki na yanar gizo, da samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba da sauransu, da inganta aikin kawo sauki ga zuba jari da yin cinikayya da yin hadin gwiwa, da tabbatar da samar da kayayyaki, da kuma yin kokarin kafa bankin raya kungiyar SCO. Na uku, a mai da hankali ga tinkari hadarin da ake fuskanta, wato kara yin hadin gwiwa wajen dakile yunkurin ‘yan ta’adda da ‘yan aware da masu tsattsauran ra’ayi, da gaggauta gina cibiyar tinkarar barazanar tsaro da kalubale, da cibiyar yaki da miyagun kwayoyi da sauransu. Na hudu kuma, a kara yin mu’amala a tsakanin jama’ar kasashe membobin kungiyar bisa bukatunsu. (Zainab Zhang)