Amurka na matsawa Isra’ila lamba game da inganta yanayin jin kai a Gaza
2024-10-16 10:13:19 CMG Hausa
Gwamnatin Joe Biden ta Amurka ta tabbatar da cewa, sakatarorin harkokin waje da na tsaron kasar, sun rattaba hannu kan wata wasika da suka aikewa takwarorinsu na Isra’ila a ranar Lahadi, inda a ciki suka bukaci Isra’ila ta inganta yanayin jin kai a Gaza, cikin kwanaki 30 masu zuwa.
Yayin wani taron manema labarai a jiya Talata, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Mathew Miller, ya tabbatar da cewa, an aike da wasikar da sakataren harkokin waje Antony Blinken da na tsaro Lloyd Austin suka rattabawa hannu zuwa ga ministan tsaron Isra’ila Yoav Gallant da ministan yayata manufar kasar, Ron Dermer.
A cewar wani rahoton CNN, wasikar ta gargadi Isra’ila cewa, idan ta gaza bayar da damar shigar da kayayyakin agaji ga al’ummar Gaza, to za ta fuskanci hadarin keta dokar Amurka game da bayar da tallafin soji ga kasashen waje. A don haka, tallafin soji da Amurka ke ba Isra’ila na cikin hadari.
Wa’adin kwanaki 30 da Amurka ta bayar na nufin idan Isra’ila ba ta dauki mataki don gane da gargadin ba, to za ta ga sakamakon hakan bayan babban zaben Amurka. (Fa’iza Mustapha)