logo

HAUSA

MOFA: Kasar Sin za ta ci gaba da karfafa hadin gwiwar samar da abinci tare da sauran bangarori

2024-10-16 19:19:44 CMG Hausa

Ranar 16 ga watan Oktoba ita ce ranar abinci ta duniya, taken ranar a bana shi ne “Wadatar abinci ga kowa da kowa, da samar da ingantacciyar rayuwa da kuma kyakkyawar makoma ga kowa”.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a wannan rana cewa, kasar Sin ta kuduri aniyar ci gaba da karfafa hadin gwiwar tabbatar da wadatar abinci tare da dukkan bangarori, da gina duniya marasa yunwa.

Mao Ning ta kara da cewa, kasar Sin ita ce kasar da ta fi kowace kasa samar da hatsi a duniya, inda take samar da kusan kashi daya bisa hudu na yawan hatsin duniya da kasa da kashi 9 cikin dari na filayen noma na duniya, tare da samar wa mutane sama da biliyan 1.4 isasshen abinci. A sa'i daya kuma, kasar Sin ta mai da hankali sosai kan batun wadatar abinci a duniya. A cikin 'yan shekarun nan, kasar Sin ta ci gaba da ba da agajin abinci na gaggawa ga kasashen da suka fuskanci bala’u daga indallahi da matsalolin jin kai, tare da raba fasahohin aikin gona, da taimakawa kasashe masu tasowa wajen inganta karfin samar da abinci. (Yahaya)