logo

HAUSA

TCN ya ce ya samu nasarar dawo da hasken wuta a fadin Najeriya

2024-10-16 09:20:59 CMG Hausa

Kamfanin dakon wutan lantarki na tarayyar Najeriya ya ce, ya samu nasarar dawo da wuta a kasar bayan lalacewar da ta yi  na tsawon sama da sa’o’i 24.

Cikin wata sanarwa dauke da sa hannu mai magana da yawun kamfanin Mrs Ndidi Mbah ta yi bayani cewa ya zuwa yammacin jiya Laraba 15 ga wata, an samar da wuta a kaso 90 na tasoshin rarraba wuta dake kasar.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Wannan dai shi ne karo na 7 a tsakanin shekara guda da aka samu katsewar wutar lantarki a dukkan fadin Najeriya, domin dai ko a ranar 14 ga watan Oktobar wannan shekara sai da daukacin al’ummar suka kasance cikin duhu na tsawon sa’o’i 24.

Kamar dai yadda yake kunshe cikin sanarwar, kamfanin ya yi bayanin cewa ana ci gaba da aikin daidaita al’amura a dukkan sauran raguwar tasoshin rarrabar wutar.

Daga cikin tasoshin da yanzu haka suka dawo aikin sun hada da na yankin Abuja.

Kakakin kamfanin dakon wutan na Najeriya ta ce, tuni aka fara aikin binciken musabbabin daukewar wutar lantarkin a gaban daya kasar.

Daukewar wutan lantarkin dai ya haifar da asarar miliyoyin naira tun daga ranar Talata zuwa Alhamis din nan. (Garba Abdullahi Bagwai)