logo

HAUSA

Kasar Sin ta kuduri aniyar ci gaba da kokarinta na tabbatar da duniyar da ba ta da makaman nukiliya

2024-10-16 19:43:53 CMG Hausa

A ranar 16 ga watan Oktoban 1964 ne kasar Sin ta yi nasarar tarwatsa bam din nukiliyarta ta farko, kuma a wannan rana ta sanar da cewa, za ta aiwatar da manufar hana fara yin amfani da makaman nukiliya.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a taron manema labaru a yau 16 ga wata cewa, tarihi da hakikanin gaskiya sun tabbatar da cewa, manufar hana fara yin amfani da makaman nukiliya, ta dace wajen kara amincewa da juna bisa manyan tsare-tsare, da sa kaimi ga kawar da makaman nukiliya, da rage hadarin da ke tattare da shi yadda ya kamata, da sa kaimi ga inganta daidaito da kwanciyar hankalin duniya. Kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da dukkan bangarori domin ci gaba da yin kokari wajen ganin an haramta da lalata makaman nukiliya gaba daya, da tabbatar da duniyar da ba ta da makaman nukiliya. (Yahaya)