logo

HAUSA

MDD ta damu da ci gaban hare-hare tsakanin Isra’ila da Lebanon

2024-10-16 10:43:00 CMG Hausa

MDD ta ce ta damu da ci gaba da kai hare hare da ake yi a iyakar wucin gadi tsakanin Lebanon da Isra’ila, inda sakatare janar na majalisar Antonio Guterres ya yi Allah wadai da asarar rayukan fararen hula da hare haren ke haifarwa.

Yayin taron manema labarai na jiya, kakakin sakatare janar din Stephane Dujarric ya ce luguden wuta a Aitou dake yankin arewacin Lebanon, ya yi sanadin mutuwar akalla mutane 23, yana mai bayyana hakan a matsayin abun damuwa ainun.

Ya kara da cewa, MDD ta damu da tasirin hakan ga fararen hula dake bangarorin biyu, musamman na Lebanon, yana mai kira ga masu ruwa da tsaki da su girmama hakkin dake wuyansu karkashin dokokin kasa da kasa, ciki har da dokar jin kai ta kasa da kasa da ta kare fararen hula.

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar (OCHA), ta ruwaito cewa, rikicin na ci gaba da raba mutane da matsugunansu, kuma hukumomi a Lebanon sun ce batun ya shafi mutane miliyan 1.2. Zuwa ranar 13 ga watan Oktoba, hukumar kula da kaura ta duniya ta ce mutane 740,000 ne suka rasa matsugunansu dalilin ta’azzarar rikici a Lebanon. (Fa’iza Mustapha)