Yaya abota da al'ummar kasar Sin take?
2024-10-16 07:15:22 CGTN Hausa
Abota tsakanin jama'a ita ce ginshikin dorewar dangantakar kasa da kasa kuma na dogon lokaci, kuma wani karfi ne mai dorewa wajen bunkasa zaman lafiya da ci gaban duniya. A cikin shekaru 75 da suka gabata tun bayan kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin (JKS) ta hada kai tare da jagorantar al'ummar Sin wajen shimfida hanyar zamanantar da jama'a, wanda ba wai kawai kasar kanta ta samu ci gaba ba, har ma da duniya baki daya.
Idan aka yi la'akari da wannan tafiya, zamu fahimci cewa nasarar da kasar Sin ta samu tana da nasaba da huldarta da sauran kasashe. Kasar Sin da abokanta a fadin duniya sun yi ta fama da bala'u iri-iri, kuma sun shawo kansu tare. Kamfanoni da cibiyoyi da kuma daidaikun jama'a da dama na kasashen waje sun taka rawar gani wajen ciyar da zamanantar da tsarin gurguzu na kasar Sin gaba, ta yadda za su samu moriyar juna, da ba da muhimmiyar gudummawa wajen inganta mu'amalar sada zumunta da hadin gwiwa tsakanin Sin da sauran kasashe. Wannan na daga cikin jawabin shugaba Xi Jinping a ganawarsa da baki na kasashen waje da suka halarci taron sada zumunta na kasa da kasa na kasar Sin da taron bikin cika shekaru 70 da kafuwar kungiyar abokantaka ta jama'ar kasar Sin da kasashen waje wato CPAFFC a ranar Juma'a.
Tsarin mu’amalantar kasashen duniya na kasar Sin yana taka muhimmiyar rawa wajen zurfafa yin gyare-gyare da kuma ciyar da zamanantar da kasar gaba a wannan sabon zamani, hakan ya sanya take kiyaye muhimman ka'idoji, da samar da sabbin damammaki, da sa kaimi ga ci gaban bil Adam. Kana huldar dake tsakaninta da sauran kasashen duniya na dauke da nufin wanzar da zaman lafiya a duniya, da sa kaimi ga samun bunkasuwa tare, da yin hadin gwiwa, da samun moriyar juna, da kawar da shakkun sauran kasashen duniya game da tsarinta na samun bunkasuwar duniya, da ba da gudummawa wajen yin mu'amalar wayewar kai. (Sanusi Chen, Saminu Alhassan, Mohammed Yahaya)