logo

HAUSA

Kasashen Indiya da Canada sun kori jami’an diflomasiyyar juna

2024-10-15 11:15:07 CMG Hausa

A jiya Litinin ne gwamnatin kasar Indiya ta bukaci jami’an diflomasiyyar kasar Canada su 6 dake birnin New Delhi da su fice daga kasar nan zuwa ranar Asabar, bayan ta yanke shawarar janye babban kwamishinanta Sanjay Kumar Verma, da wasu manyan jami’an diflomasiyya, da ma’aikata daga kasar ta Canada.

A nata bangare, ita ma kasar Canada ta bayyana korar jami’an diflomasiyyar Indiya su 6, ciki har da babban kwamishina.

Lamarin dai ya biyo bayan zargin da Canada ta yi cewa babban kwamishinan ofishin diflomasiyyar Indiya, da wasu jami’an jakadancin kasar dake Canada na cikin wadanda ake bincike, don gane da wasu batutuwa da suka shafi kasar, zargin da Indiya ta yi matukar bayyana adawa da shi. (Saminu Alhassan)