logo

HAUSA

Firaministan kasar Sin ya gana da shugaban Pakistan da firaministan Kyrgyzstan

2024-10-15 21:41:01 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Qiang ya bayyana a yau Talata cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da Pakistan wajen kiyaye mu’amala tsakanin manyan jami’ai, da kuma nuna goyon baya ga juna kan batutuwan da suka shafi muhimman muradunsu.

Li ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da shugaban Pakistan Asif Ali Zardari.

Hakazalika, firaminista Li Qiang ya gana da firaministan kasar Kyrgyzstan Akylbek Zhaparov a gefen taron majalisar shugabannin gwamnatocin kasashe mambobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai karo na 23 da aka gudanar a yau Talata. Inda Li ya bayyana cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da Kyrgyzstan wajen tabbatar da hadin gwiwa a tsakaninsu, da ci gaba da zama aminai kuma amintattun abokan hadin gwiwa, wajen raya kasa, da kara ciyar da shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” gaba tare. (Yahaya)