logo

HAUSA

Jirgin ruwan ba da agajin kiwon lafiya na rundunar sojan ruwan kasar Sin ya kammala ziyara a Kamaru

2024-10-15 10:39:06 CMG Hausa

A jiya Litinin 14 ga watan nan ne jirgin ruwan ba da agajin kiwon lafiya na rundunar sojojin ruwan kasar Sin mai suna "Peace Ark", wanda ke gudanar da aikin da aka yiwa lakabi da "Harmony Mission-2024", ya tashi daga tashar jiragen ruwa ta Douala, bayan yin nasarar kammala ziyararsa ta farko a Kamaru, ya kuma nufi kasar Benin, zango na goma na wannan aiki.

A yayin ziyarar sada zumunci ta kwanaki 7 a Kamaru, jirgin ruwan na "Peace Ark", ya ba da hidimar kiwon lafiya ga mutane sama da 6,800, tare da gudanar da binciken lafiya na taimako ga mutane kusan 3000, wanda ya samu kyakkyawar tarba da yabo daga jama'ar Kamaru.

Haka zalika, wakilan hafsoshi, da sojoji sun je jami'ar Douala, da sauran wasu wurare domin ba da lakcoci na ilimin kiwon lafiya, da musayar al'adu, kana da gudanar da wasan kwallon kafa na sada zumunta tare da jami'ai da sojojin Kamaru, wanda ta hakan aka kara fahimtar juna, da zurfafa zumunci tsakanin bangarorin biyu. (Bilkisu Xin)