Sin na son kiyaye bude kofa da yin hadin gwiwar kimiyya da fasaha don amfanawa duniya
2024-10-15 20:01:14 CMG Hausa
Hukumar ikon mallakar fasaha ta duniya ta gabatar da rahoto kan yin kirkire-kirkire a fadin duniya na shekarar 2024 a kwanakin baya, inda aka shaida cewa, karfin yin kirkire-kirkire na kasar Sin yana a matsayi na 11 a duniya, karuwar matsayi 1 bisa na shekarar bara, kana ta kasance kasa daya tilo mai matsakaicin kudin shiga a cikin kasashe 30 dake kan gaba a jerin sunayen. Game da wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a yau cewa, yin kirkire-kirkire kan kimiyya da fasaha a kasar Sin yana amfanawa kasar Sin, har ma da sassan duniya, Sin tana son kiyaye yin hadin gwiwar kimiyya da fasaha ta hanyar bude kofa da amincewar bambance-bambance a sassan duniya.
Mao Ning ta bayyana cewa, Sin ta inganta karfinta na yin kirkire-kirkire ta hanyar zuba jari ga yin nazarin kimiyya da fasaha da hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa ta hanyar bude kofa da amincewa da bambance-bambance. An ce, yawan kudin da aka zuba kan nazarin kimiyya da fasaha a kasar Sin a shekarar bara ya zarce kudin Sin Yuan triliyan 3.3, wanda ya karu da kashi 8.4 cikin dari bisa na shekarar 2022. Ban da wannan kuma, Sin ta kafa dangantakar hadin gwiwar kimiyya da fasaha tare da kasashe da yankuna fiye da 160, da daddale yarjejeniyoyin hadin gwiwar kimiyya da fasaha a tsakanin gwamnatocin kasa da kasa guda 118. Yanayin yin kirkire-kirkire da albarkatun kwararru a kasar Sin sun kara jawo kamfanonin kasa da kasa da su zo kasar Sin su kafa cibiyoyin nazari. (Zainab Zhang)