Dangantakar Sin da Nijar a fannin kiwon lafiya na kara inganta
2024-10-15 15:14:07 CMG Hausa
A wajen bikin kaddamar da taron kolin dandalin tattauna hadin-kan Sin da Afirka wato FOCAC da aka yi a watan Satumbar bana a Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da wasu muhimman matakan hadin-gwiwa guda 10 don zamanantar da Sin da Afirka, ciki har da matakin inganta harkokin kiwon lafiya.
Dangantakar kasar Sin da Jamhuriyar Nijar ta fuskar kiwon lafiya na da dogon tarihi. Tun daga shekara ta 1976, jihar Guangxi ta kasar Sin ta fara tura ma’aikatan jinya zuwa Jamhuriyar Nijar, kuma ma’aikatan jinyar kasar Sin guda 30 dake aiki a wurin a halin yanzu, suna cikin tawagar ma’aikatan jinya na kasar Sin kashi na 24, wadanda suka tashi a ranar 8 ga watan Yunin shekarar da muke ciki zuwa Nijar, inda za su samar da tallafin jinya ga mazauna kasar na tsawon shekara daya da rabi.
“Ciwon hakori ya dame ni, ya kai wajen kwana nawa, watanni ma. An ce min likitocin China suna duba marasa lafiya kyauta, shi ya sa muka taho nan don ganin likita. An duba mana an rubuta mana magunguna an rubuta mana radio an ba mu rendez-vous(appointment), wanda za mu dawo. Akwai na’urori masu kyau.”
Maganar da kuka ji dazu, magana ce daga bakin Madam Jamilah, daya daga cikin marasa lafiya da suka je ganin likitan kasar Sin a babban asibitin Nijar dake birnin Yamai. Kamar ita Jamilah, a kan samu ’yan Nijar da dama da sukan je neman ganin likitocin kasar Sin a asibitin a kowace rana, musamman lokacin da aka shirya aikin duba marasa lafiya kyauta. Babban asibitin Nijar dake Yamai, shi ne wurin da tawagar ma’aikatan jinya ta kasar Sin kashi na 24 ke aiki, inda likitocin kasar Sin ke hada kai tare da likitocin Nijar, don samar da jinya ga marasa lafiya.
Liang Quanjiang, daya ne daga cikin likitocin kasar Sin dake aiki a babban asibitin Nijar dake birnin Yamai a halin yanzu. Ya ce, abun da ya burge shi, shi ne yadda al’ummar Nijar ke yi wa likitocin kasar Sin karamci da godiya:
“Jama’ar Nijar mutane ne masu kirki, wadanda ke mana karamci sosai, musamman marasa lafiya da suka zo wajen mu, su kan yi mana godiya. Idan mun kammala yi musu aikin tiyata, su kan ce mana ‘na gode na gode’, kuma cike suke da hawaye. Da muka zo nan, ’yan Nijar, ko sun san ka ko ba su san ka ba, ko ma’aikata, ko kuma masu wucewa a titi, su kan gaishemu.”
Dokta Liang ya ce, aikin samar da jinya a Nijar ya bambanta da aikin da suke yi a kasar Sin, saboda akwai wasu cututtuka ko kuma nau’ikan kwayoyin cuta a Nijar, da ba’a yawan ganinsu a kasar Sin, al’amarin dake bukatar hadin-gwiwar likitocin Sin da Nijar sosai, inda ya ce:
“Kamar cutar amosanin jini, ba’a yawan ganin ta a kasar Sin, amma a Nijar ana samun ta, har ma an kafa wata cibiya don nazarinta. Kana, mu kan nazarci abubuwan da aka riga aka wallafa su a kafafen yada labarai ko cikin rahotanni, da kuma tattaunawa tare da likitocin Nijar don cimma matsaya kan yadda za mu samar da jinya yadda ya kamata ga marasa lafiya. Game da cututtuka masu yaduwa kuma, likitocin Nijar suna da kwarewa sosai wajen shawo kan su, musamman kamar cutar kafafu. Idan wani mutum bai sanya takalma ba har ya shiga ruwa mara tsafta, ya kan kamu da kwayar cutar da ta shafi kafafu. Duk wadannan cututtukan dake yawan damun jama’ar Nijar, mu kan tattauna kansu tare da likitocin kasar, don shawo kansu cikin hadin-gwiwa.”
Dokta Liang ya kuma ce, gudanar da aiki tare da likitocin Nijar ya sa ya kara fahimtar kwarewar su ta fuskar kulawa da marasa lafiya, inda ya ce:
“Kwarewar likitocin Nijar ta wuce tsammanina. Da ma a nawa ra’ayi, aikin jinya a nan, a baya yake, kuma likitoci ba sa mu’amala da na sauran kasashe, ko kuma ba su samu horo sosai ba. Amma gaskiya ba haka ba ne. Akwai likitocin Nijar da dama, wadanda suka taba yin karatun likitanci a kasashen waje, ciki har da kasar Sin. Kamar akwai wani likita, yana da digiri na biyu a fannin likitanci.”
Sunan likita mai digiri na biyu a fannin likitanci da Dokta Liang ya ambata, shi ne Abdallah, wanda ya taba yin karatu bisa kyautar kudin karatu da ya samu a wata jami’a dake birnin Jiamusi na lardin Heilongjiang dake arewa maso gabashin kasar Sin. Dokta Abdallah ya kwatanta ayyukan jinya da suke yi a Nijar da kasar Sin, inda ya ce:
“Yanzu gaskiya aiki a nan ba wata babbar matsala. Akwai mutane, kuma akwai na’urorin aiki, babu wani babban bambanci da na can wajen da nan wajen. Ana iya samun bambanci a bangaren cututtuka. Amma idan aka dauki misalin cutar kansa, can wajen ana yin surgery na cutar kansa da yawa, amma nan wajen namu, ba mu yin su kamar yadda ake yin su can, nan kadan ne. Kuma a nan, marasa lafiya ba sa saurin zuwa asibiti, su kan dauki tsawon lokaci kafin zuwa. In sun zo ma, dukka sai kun gani late suke zuwa.”
Dokta Abdallah ya ce yana jin dadin aiki tare da likitocin kasar Sin, kuma yana son sake dawowa kasar in akwai dama:
“Muna mu’amala tare, mu’amalar kwarai ce muke tare da su gaskiya. Ni yanzu China ma kaman dai, kasa ta ce ta biyu, in na samu kuma, ina so in koma can.”
Abu na daban dake jan hankalin marasa lafiya na Nijar a babban asibitin Nijar dake Yamai, shi ne likitanci da maganin gargajiya na kasar Sin.
A dakin samar da jinya bisa likitancin gargajiya na kasar Sin a asibitin, Hajiya Fatimah, wadda ke fama da ciwon baya, ta ce:
“Yau dai ne na zo, na samu labari. Wata ta kawo ni nan, ita ma tana nan. Ta ce ita ta taba yi, ta ce ta ji dama.”
Daya daga cikin likitocin dake amfani da fasahohin gargajiya na kasar Sin don kulawa da marasa lafiya a asibitin, ya bayyana cewa, akwai marasa lafiya da dama, kamar ita Hajiya Fatimah, wadanda suka amince da likitancin gargajiya na kasar Sin, bayan da su kansu ko kuma abokanansu suka samu sauki sakamakon jinyarsu da aka yi bisa likitancin gargajiyar kasar Sin, inda ya ce:
“Akwai wata dalibar jami’a mai shekaru 20 da wani abu, wadda ta dade tana fama da ciwon kugu, har da ciwon kafafu. An yi jinyarta har fiye da shekara daya, amma ba ta samu sauki ba. Sai ta zo wajen mu, inda muka caccaka allurai a cikin fatan jikinta fiye da sau 10 wato fasahar acupuncture, da ba ta magungunan gargajiyar kasar Sin don ta sha, kuma ta samu sauki sosai, har ta rubuta mana wasikar godiya.”
Sakamakon matukar kokarin da ma’aikatan jinyar kasashen Sin da Nijar suka yi cikin hadin-gwiwa, harkokin kiwon lafiya a Nijar na inganta, kuma marasa lafiya da dama suna samun sauki. Amma masu iya magana kan ce, rigakafi ya fi magani. Likitocin Sin da Nijar dake aiki a wannan asibiti, su ma suna daukar matakai iri-iri domin fadakar da al’umma kan muhimmancin rigakafi gami da shawo kan cututtuka iri-iri, musamman masu yaduwa.
Dokta Liang Quanjiang ya ce:
“A ’yan kwanakin nan, cutar kyandar biri na yaduwa a wasu kasashen Afirka. Mu ma mun karanci bayanai da dama, don kara ilimi kan wannan cuta, kuma muna shirin kafa wasu alluna don fadakar da al’umma kan matakan rigakafin cutar, har ma ta hanyar kafafen yada labarai. Za mu yi iyakacin kokari don ilmantar da al’ummar kasar yadda za su tinkari cututtuka iri-iri.”
Shi ma Dokta Abdallah ya yi kira ga ’yan kasar sa, musamman masu fama da rashin lafiya, da kada su bata lokacin wajen zuwa ganin likita da wuri, inda ya ce:
“In dai mutum ya ji ba ya da lafiya, ya gaggauta ya zo ganin likita, ba zama za ka yi a gida ba, ba sai babu yadda za ka iya kuma sa’annan mutum zai zo wajen likita ba, a’a. Da ka ji dai wurin ba ka jin lafiya, akwai inda ke damunka, sai ka zo ganin likita tun da wuri.” (Murtala Zhang)