logo

HAUSA

Kashim Shettima: Najeriya ba za ta samu ci gaba mai dorewa ba ta hanyar dogaro kawai a kan man fetur

2024-10-15 09:43:23 CMG Hausa

Mataimakin shugaban tarayyar Najeriya Sanata Kashim Shettima ya bayyana damuwarsa a bisa yanayin matsayin rayuwa da ake fuskanta yanzu haka a kasar sakamakon sauye-sauyen manufofin tattalin arziki.

Ya bayyana hakan ne ranar Litinin 14 ga wata a birnin Abuja yayin babban taro kan tattalin arzikin kasa karo na 30 da aka bude. Ya ce, shi da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu suna matukar tausayawa ’yan kasa a game da halin da ake ciki, amma ya ce wahalar ba za ta ci gaba da dorewa ba.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Sanata Kashim Shettima ya ci gaba da cewa, duk da kalubalen da yanzu haka al’umma ke fuskanta a kasar, wannan dai ba zai hana gwamnati ci gaba da aiwatar da sauye-sauyenta ba a kan manufofin tattalin arziki saboda muhimmancinsa ga samun nasarar dorewar ci gaban kasa.

Ya ce, suna sane da mawuyacin halin da masu karamin karfi da matasa ke ciki, amma dai ya zama wajibi a yi kokarin dora kasar bisa ingantacciyar turba da za ta kai ga bunkasuwar tattalin arziki a kowane mataki.

Mataimakin shugaban kasar ya ce, sanin kowa ne cewa tattalin arzikin Najeriya ya tabarbare matuka saboda dogaro da aka yi kachokan a kan man fetur, wanda kuma ba ya iya samar da guraben aikin yi ga miliyoyin al’ummar kasa.

A sakamakon hakan ne Sanata Kashim Shettima ya ce, yanzu haka gwamnati ta karkatar da hankalinta sosai a kan wasu bangarorin tattalin arziki musamman bangaren aikin gona, masana’antu da kuma bangaren fasahohin zamani, baya ga haka kuma tuni gwamnati ta bullo da tsare-tsaren tallafawa masu kanana da matsakantan masana’antu domin su bunkasa harkokinsu, inda ya bayyana babban taron tattalin arziki karo na 30 a matsayin wani dandali da zai fito da managartan shawarwari a kan yadda al’amura za su daidaita a cikin dan kankanen lokaci. (Garba Abdullahi Bagwai)