logo

HAUSA

Sin ta fitar da shirin bunkasa ayyukan kimiyyar sararin samaniya na shekarar 2024 zuwa 2050

2024-10-15 14:53:13 CMG Hausa

A yau Talata ne kasar Sin ta fitar da wani sabon shirin bunkasa ayyukan kimiyyar sararin samaniya na kasa, wanda ya kunshi ayyukan da za a gudanar a matsakaici da dogon zango don raya fannin.

Cibiyar nazarin kimiyya ta kasar Sin ko CAS, da hukumar kula da ayyukan harba kumbuna ta kasar, da hukumar kula da ayyukan harba kumbuna masu dauke da 'yan sama jannati ta kasar ne suka fitar da sabon shirin, wanda zai ja ragamar kasar ta fannin tsare tsaren ayyukan kimiyyar sama jannati, da binciken samaniya, tun daga shekarar nan ta 2024 har zuwa 2050.

Shirin wanda shi ne irin sa na farko a matakin kasa, an kaddamar da shi ne yayin wani taron manema labarai, wanda ofishin watsa labarai na majalissar gudanarwar kasar Sin ya shirya.

Kaza lika karkashin shirin, an fayyace manufofin da ake fatan cimmawa a fannin ayyukan kimiyyar sararin samaniya na Sin, ciki har da manyan manufofi da suka shafi sassa 17, karkashin manyan ginshikan kimiyya 5, da kuma wasu tsare tsare masu zango uku-uku. (Saminu Alhassan)