Ministan wajen Najeriya ya kira mukaddashin jakadan Libya game da yadda tawagar Super Eagles ta makale a filin jirgin saman kasar
2024-10-15 15:25:22 CMG Hausa
Ministan harkokin wajen tarayyar Najeriya Yusuf Maitama Tuggar ya kira mukaddashin jakadan kasar Libya dake kasar, don jin bahasin yadda tawagar Super Eagles ta ’yan wasan Najeriya ta makale a filin jiragen saman Libya har tsawon sa’o’i 12.
Tawagar ta Super Eagles ta isa kasar Libya a ranar Lahadi, domin buga wasa na biyu na neman gurbin buga gasar cin kofin nahiyar Afirka na shekarar 2025 dake tafe, bayan da ta doke Libya a wasan farko da suka buga da ci 1 da nema, a jihar Akwa Ibom ta kudancin Najeriya a ranar Juma’ar makon jiya.
Rahotanni daga tawagar ta Super Eagles na cewa, sun yi hayar jirgin da aka tsara zai sauka a birnin Benghazi, amma ba zato ba tsammani sai aka karkatar da jirgin zuwa filin jiragen sama na kasa da kasa na Al Abraq, wanda ke karbar jiragen dake sauka birnin Bayda na gabashin kasar, daga nan ne kuma aka bar ’yan wasan tsawon sa’o’i masu yawa.
Sakamakon faruwar hakan, a cewar Yusuf Tuggar, an umarci ’yan wasan tawagar ta Super Eagles da kada su buga wasan da ya kai su kasar.
Wata sanarwar ta daban kuwa, wadda aka wallafa a shafin X, ta rawaito kyaftin din tawagar ta Super Eagles William Troost-Ekong na cewa, ’yan wasan na Najeriya sun fuskanci tozarci, kana sun gaji matuka sakamakon yanayi maras dadi da aka bar su a ciki, don haka suka yanke shawarar kin buga wasan da ya kai su Libya, kuma hukumar kwallon kafar Najeriya NFF ta amince da matakin da suka dauka.
A wani ci gaban kuma, wani jami’in hukumar NFF, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar tarho cewa, da jin labarin abun da ya auku, sai aka tsara dawo da tawagar ta Super Eagles gida, domin kare lafiya da tsaron ’yan wasan. (Saminu Alhassan)