Sin ta kalubalanci Amurka da ta dakatar da kai hari ta yanar gizo a fadin duniya
2024-10-14 21:17:09 CMG Hausa
Cibiyar lura da manhajoji masu cutar da na’ura mai kwakwalwa, da hadin gwiwar dakin gwaje-gwajen kasar Sin na binciken fasahar yaki da manhajoji masu cutar da na’ura mai kwakwalwa, da kamfanin 360 na kasar Sin sun fitar da rahoto a kwanakin baya, inda suka ce, Amurka ta kara gishiri kan labaru masu nasaba da wata kungiya mai suna "Volt Typhoon" ne a yunkurin zargin wasu kasashe da kuma boye matakanta na kai hari ta yanar gizo.
Game da wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, hukumomin Sin da abin ya shafa sun riga sun gabatar da rahotanni biyu kan batun, inda aka bayyana cewa, hukumar leken asiri ta Amurka da kamfanonin tsaron yanar gizo na Amurka sun yi amfani da kungiyar "Volt Typhoon" don samun kudin jarin da majalisar dokokin Amurka ta bayar, da sa hannu kan kwangilar gwamnatin, da yada labarai marasa tushe don zargin kasar Sin.
Mao Ning ta yi nuni da cewa, rahoton da aka bayar a wannan karo ya shaida cewa, Amurka ta yi amfani da hanyoyin fasahohin zamani don boye harin da ta kaiwa wasu kasashe ta yanar gizo, kana ta yi amfani da fifikonta na layin sadarwa karkashin teku don sa ido da leken asirin sassan duniya, da kiyaye leken asiri kan kasashen kawayenta ciki har da kasar Jamus, da kuma maida wasu manyan kamfanonin kimiyya da fasaha na kasar da su taimakawa cimma yunkurin gwamnatin Amurka. (Zainab Zhang)