Yang Tuan dake mayar da hankali kan kyautata zaman rayuwar manoma
2024-10-14 21:20:20 CMG Hausa
A fannin jin dadin jama’a da ba da agaji a kasar Sin, Yang Tuan ta kasance wata mace da ba za a iya tserewa ba. Ta dade tana mai da hankali kan bincike kan manufofin zamantakewa, da suka shafi ba da tabbaci a bangaren zamantakewa, da ba da agajin jin kai da jin dadin jama’a, da cikakkun kungiyoyin hadin gwiwar manoma, da kuma kulawa na dogon lokaci ga tsofaffi da dai sauransu. Manufofi da shawarwarin da ta gabatar, sun fito ne dogaro da binciken halin da manoma suke ciki.
Yang Tuan, mai shekaru 75, farfesa ce a sashen nazarin zamantakewa da al’umma na jami’ar cibiyar nazarin ilmomin kimiyyar zamantakewa ta kasar Sin, wadda ta fito daga dangin juyin juya hali.
Tun daga shekarar da ta kammala karatu a makarantar firamare, duk lokacin hutun yanayin zafi, iyayenta kan bar Yang Tuan ta zauna a karkara na wani dan lokaci, tun daga kwanaki sama da goma zuwa wata guda, inda take cin abinci, da hutawa, har ma da yin aiki a gonaki tare da manoman wurin.
Yayin da ta kai shekaru 19 da haihuwa, Yang Tuan ta amsa kiran kasar Sin, inda ta tafi gandun noma dake lardin Yunnan dake kudu maso yammacin kasar. Manoman wurin sun gabatar da gida mafi kyau domin ta zauna a ciki. A cikin shekaru uku da rabi na zamanta a gandun noma a Yunnan, Yang Tuan ta dorawa kanta yin ko wane irin aiki. A nan, ta koyi yadda ake noma, shuka ciyayi, yankan shinkafa, har ma ta koyi yadda ake suyar abinci a tukunya mai fadi a babban dakin cin abinci, da kuma kula da kananan yara a gidan renon yara.
Yang Tuan ta ce, komai na iya yin girma a kasa mai cike da karfin rayuwa, ciki har da manufofin zamantakewa, jin dadin jama’a, da kuma ayyukan kula da tsofaffi.
A shekara ta 2001, Yang Tuan ta je birnin Yan’an na lardin Shan’anxi, domin yin nazari da dubawa, inda ta gano cewa gine-ginen da ke wurin suna nan kamar yadda suke a shekarun da suka gabata. Yang Tuan ta ji cewa tana da alhaki, da nauyi na yin wani abu ga Yan’an.
A wancan lokacin ta gudanar da cikakken bincike kan tattalin arziki, da jin dadin jama’a, da sauran al’amura na yankunan karkara na Yan’an, inda ta gano cewa yana da wahala, da tsada ga manoman wurin su samu magani, kuma talauci da rashin lafiya ke haifarwa al’amari ne da ya zama ruwan dare.
A shekara ta 2002, Yang Tuan ta fara aikin gwajin hadin kai kan kiwon lafiya na farko a gundumar Luochuan ta birnin Yan’an. Tun daga lokacin, ba ta sake barin karkara da manoma ba.
A wancan lokacin, kasar Sin ta fitar da wata sabuwar takardar kiwon lafiya ta hadin gwiwa, inda ta bukaci kowane manomi ya biya RMB yuan 10. Amma ba a yi amfani da wannan kudi wajen magance kananan cututtuka ba, sai dai don magance manyan cututtuka. Amma saboda ba kullum ake iya samun cututtuka masu tsanani ba, don haka manoma ba su son biyan kudin sakamakon rashin samun moriya nan da nan.
Yang Tuan ta fahimci cewa, a yayin da ake aiwatar da manufofi, dole ne a tsaya daga matsayin manoma, da kuma sauraron muryoyinsu, da kuma kyautatawa, da daidaita manufofi bisa ainihin bukatunsu. Don haka, yayin da take ba da shawarwarin yanke shawara, ta himmatu wajen karfafa gwiwar manoma da su shiga cikin tattaunawar, tare da jan hankalin su wajen yin kokari ba kawai don cimma muradun tattalin arzikinsu ba, har ma da daukar nauyin dake bisa wuyansu kan zamantakewa, da ma neman samun wadata tare.
Bayan yin cudanya sau da yawa, manoman sun amince da shirin da Yang Tuan ta gabatar, wato a hada kai da cibiyar kula da lafiya ta gari. Bayan manoman sun biya kudin, za su baiwa cibiyar kula da lafiya, cibiyar kuma za ta kafa tashoshin kula da lafiya na al’umma a kauyuka daban daban, inda duk manoman da suka biya za su ji dadin rangwamen farashin magunguna har kusan kashi 50 cikin dari bisa ga farashin kasuwa. Tashoshin kuma za su samar da hidimomi na gida-gida, hidimar tuntubar juna, ba da jinya kyauta da dai sauransu. Irin wannan shiri ya samu goyon baya kwarai da gaske daga wajen manoma, inda yawan wadanda suka biya kudi ya kai kashe 90 cikin dari da wani abu.
Sai dai kuma ba zai yiwu a dogaro da manoma kadai ba wajen biyan kudaden ayyukan kiwon lafiyar al’umma, a wancan lokacin ma gwamnati ba ta da isassun kudi don gudanar da ayyukan.
Tun daga wannan lokacin, Yang Tuan ta fahimci cewa, bunkasuwar hadin gwiwar tattalin arziki a yankunan karkara ita ce hanyar da ta dace ta magance matsalar albarkatun hadin kan kiwon lafiya.
A shekarar 2005, Yang Tuan ta kafa kungiyar hadin kai ta manoma, don taimakawa manoma wajen gudanar da harkokin tattalin arziki cikin hadin gwiwa.
Domin tabbatar da shirin kasa bisa manyan tsare-tsare na farfado da yankunan karkara, kungiyar ta daddale yarjejeniya tare da manoman wurin. Bisa ga yarjejeniyar, kungiyar za ta gudanar da harkokin aikin gona baki daya kan yankunan kasa masu fadin hekta 8000. Haka nan za su tattara kayan noma kamar su wake, da kayan lambu da manoma da kansu suke nomawa, don sayar da su a kantunan da kungiyar ta kafa, ta yadda hakan zai baiwa manoman damar kara samun kudin shiga yadda ya kamata.
A ganin Yang Tuan, ayyukan da suka shafi manoma, da sha’anin noma, da yankunan karkara da kuma ayyukan jin dadin jama’a, ayyuka ne da ya kamata a rika yadawa daga zamani zuwa zamani. Don haka, tana mayar da hankali sosai kan horar da matasa.
Tun daga shekarar 2012, kungiyar hadin kai ta manoma ta fara gudanar da wani aikin horar da kwararru, da nufin horar da matasan da za su gudanar da aiki a al’ummomin yankunan karkara. Yang Tuan na fatan jagorantar matasan don fadada tunaninsu, da kuma tallafawa da taimaka musu wajen samun ci gaba.
Yang Tuan tana da shekaru 75 a wannan shekara, kuma tana tunanin za ta iya yin aiki har zuwa shekaru 80 ko 85, tana son ci gaba da aiki tare da matasa, don ganin sauye-sauyen da ake samu a yankunan karkara tare.