logo

HAUSA

Yaushe ne za a fitar da Sama Tabeel daga fargaba

2024-10-14 22:10:08 CMG Hausa

Daga Lubabatu Lei

Sakamakon matakan soja da Isra’ila ta fara daukawa tun watan Oktoban bara, Palasdinawa sama da miliyan biyu aka raba da muhallansu a zirin Gaza, ciki har da yarinya mai suna Sama Tabeel da iyalanta.

Wata rana da daddare, sojojin Isra’ila sun kai hari inda Sama da iyalanta ke gudun hijira a yankin Rafah, amma Sama da iyalanta sun taki sa’a sun tsira daga fashewar bama-bamai da wargajewar gine-gine, kuma kashegari sun bar Rafah sun tashi zuwa Khan Younis. Amma sakamakon tsananin gigita Sama da harin ya yi, gashin kanta ya fara zubewa. Duk da cewa iyayenta sun yi iyakacin kokarin neman mata magani, amma sun gaza, sakamakon yadda ake matukar fuskantar matsalar karancin magani da likita a Gaza.

Sama da shekara guda ke nan da barkewar rikici a tsakanin Palasdinu da Isra’ila, amma maimakon kurar rikicin ya lafa, sai kara yaduwa take yi, har zuwa sauran kasashen yankin gabas ta tsakiya, ciki har da Lebanon da Syria da Iran da sauransu, lamarin da ya jefa al’ummomin kasashen cikin mawuyacin hali. Kawo yanzu, Palasdinawa sama da dubu 42 suka halaka baya ga kusan dubu 100 da suka jikkata a zirin Gaza a sakamakon rikicin, sai kuma a Lebanon, mutane sama da 2000 suka mutu baya ga wasu sama da dubu 10 suka ji raunuka… A sa’i daya kuma, fararen hula sama da dubu daya suka jikkata a Isra’ila, a yayin da daruruwan sojojin kasar suka halaka.

Kamata ya yi bangarorin da rikicin ya shafa da ma gamayyar kasa da kasa su yi tunani sosai a kan cewa, shin me ya haifar da tushen kiyayya da juna a shiyyar? Baya ga haka, a yayin da halin da ake ciki ke dada ta’azzara a yankin gabas ta tsakiya, kasashe da dama sun yi ta kira ga bangarori masu ruwa da tsaki da su tsagaita bude wuta, kuma sau da yawa kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya da kuma babban taron majalisar sun kira taro game da yanayin da ake ciki a zirin Gaza da Lebanon da kuma gabas ta tsakiya, don fatan ganin an tabbatar da tsagaita bude wuta. Amma ita kasar Amurka a maimakon ta yi kokarin sanyaya yanayin da ake ciki, sai ta yi ta rura wutar rikicin, wadda sau da dama ta jefa kuri’ar kin amincewa da daftarin shirin tsagaita bude wuta da aka gabatar a kwamitin sulhu na MDD, har ma ta yi ta samar da makamai ga Isra’ila, ko a karshen watan Satumba, Amurka ta kara samar da gudummawar soja da ta kai kimanin dala biliyan 8.7 ga Isra’ila. Lallai, yadda kasashen yamma suka bi ma’aunai biyu a kan batun, shi ma ya haifar da tasiri ga aukuwar rikici a yankin gabas ta tsakiya.

Abubuwan da ke faruwa a gabas ta tsakiya sun shaida cewa, daukar matakan soja da nuna karfin tuwo ba za su taimaka ga daidaita matsala ba. Abin da ake bukata wajen daidaita rikicin Palasdinu da Isra’ila shi ne niyyar siyasa da kuma daukar matakan diplomasiyya, a maimakon makamai da kuma daukar matakan takunkumi. Kamata ya yi manyan kasashe su taka rawar da ta dace, su kiyaye adalci, don kwantar kurar yaki da shawo kan yaduwar rikicin.

Ba da jimawa ba, kasar Sin ta bayar da shawarar daidaita rikicin Gaza bisa wasu matakai uku, wato na farko a gaggauta tsagaita bude wuta da samar da agajin jin kai, sa’an nan, a bi ka’idar ba Palasdinawa ikon gudanar da harkokinsu da kansu, daga karshe, shirin samar da kasashe biyu zai zama ainihin mafita ta warware matsalar. Kamata ya yi kasa da kasa su sa kaimi ga kwantar da kurar rikici, sa’an nan su tsara taswirar aiwatar da shirin, don tabbatar da zaman lafiya a tsakanin Palasdinu da Isra’ila, da Larabawa da kuma Yahudawa.

Sama da shekara guda ke nan, ba a ko taba ganin alamar zaman lafiya a Gaza ba, ga shi yanzu Lebanon ma ta tsunduma cikin yaki. Shin yaushe ne za a maido da zaman lafiya a gabas ta tsakiya? Kuma yaushe ne za a fitar da yara irinsu Sama Tabeel daga fargabar da aka jefa su a ciki? (Mai Zane: Mustapha Bulama)