logo

HAUSA

Firaministocin Sin da Vietnam sun halarci taron kara wa juna sani na wakilan kamfanonin kasashensu biyu

2024-10-14 13:58:46 CMG Hausa

 

Firaministan kasar Sin Li Qiang da takwaransa na Vietnam Pham Minh Chinh, sun halarci taron wakilan kamfanonin kasashen biyu a jiya Lahadi a birnin Hanoi.

Bayan ya saurari jawaban da wakilan suka gabatar, Li Qiang ya ce, a shekarun baya bayan nan, huldar kasashen biyu na bunkasa yadda ya kamata bisa kokarin kasashen biyu cikin hadin gwiwa, inda aka samu sakamako mai armashi. Ya kara da cewa bisa dadaddiyar abokantakar kasashe makwabta masu bin tsarin mulki na gurguzu, bunkasuwarsu ta zama kyakkyawar dama gare su.

Tattalin arziki da ciniki, muhimman bangarori ne biyu dake taimakawa hadin gwiwarsu, kuma ingantaccen karfi ne dake ingiza bunkasuwar huldar kasashen biyu. Mr. Li ya ce idan an yi hangen nesa, za a gano cewa, bangarorin biyu na ci gaba da mu’ammala kan tsare-tsaren bunkasuwarsu da kara cudanya da tuntubar juna, da kuma koyi da juna da taimakawa juna, matakan da suka samar da makoma mai haske wajen habaka hadin gwiwarsu.   

A nasa bangare, Pham Minh Chinh ya ce, bisa jagorancin shugabannin kasashen biyu, ba shakka huldar kasashen biyu za ta kara zurfafa, kana za a shiga wani sabon zamani na kafa kyakkyawar makomarsu ta bai daya. Ya ce, Vietnam na fatan kara hadin kan kamfanonin kasashen biyu bisa ruhin kawowa juna moriya, da amfani da fifikonsu da boyayyen karfinsu, ta yadda za a gaggauta hadin gwiwarsu a bangaren hada-hadar kudi, da kimiyya da fasaha, da zuba jari, da samar da manyan ababen more rayuwa, da tattalin arziki na yanar gizo, da mu’ammalar tsarin samar da hajoji da sauransu. (Amina Xu)