Neman ‘yancin kai na Taiwan tsokana ce kuma za ta gamu da matakan magance ta
2024-10-14 20:41:04 CMG Hausa
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana a yau Litinin cewa, neman ‘yancin kai na Taiwan na tada zaune tsaye a mashigin tekun Taiwan, kuma ba makawa za a dauki matakan dakile tsokanar ‘yan aware masu neman ‘yancin kai na Taiwan.
A yau Litinin ne rundunar ‘yantar da jama’ar kasar Sin PLA ta yankin gabashin kasar ta shirya sojojinta na kasa, da na ruwa, da na sama da na harba makamai masu linzami, domin gudanar da atisayen "Joint Sword-2024B" a mashigin tekun Taiwan da arewa, da kudu da gabashin yankin tsibirin Taiwan.
Da take amsa wata tambaya mai nasaba da wannan batu, kakaki Mao Ning ta shaidawa manema labarai cewa, a ko da yaushe kasar Sin ta jajirce wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, wanda kasashen dake yankin suka tabbatar da hakan. Mao ta jaddada cewa, Taiwan wani muhimmin bangare ne na kasar Sin, kuma batun Taiwan batu ne na cikin gidan kasar Sin, wanda kar a yi tsangwama daga waje.
Mao ta kara da cewa, idan da gaske Amurka ta damu da zaman lafiya da kwanciyar hankali a mashigin tekun Taiwan da wadata a yankin, kamata ya yi ta mutunta ka'idar Sin daya tak a duniya da kuma matsayar sanarwoyi guda uku na hadin gwiwar kasashen Sin da Amurka. Ta kuma himmantu kan aiwatar da kudurin shugabanninta na kin goyon bayan ‘yancin kai na Taiwan, da dakatar da baiwa Taiwan makamai, da kuma daina dora 'yan aware masu neman 'yancin kai na Taiwan kan gurguwar tunani.(Yahaya)