Babban yankin kasar Sin ba za ta dakatar da matakai ba, illa masu neman ‘yancin kan Taiwan sun daina matakan takala
2024-10-14 21:17:21 CMG Hausa
Yau Litinin 14 ga wata ne rundunar ‘yantar da al’umma ta kasar Sin ko PLA yankin gabashi ta gudanar da atisayen hadin gwiwa na sojojin kasa, da na ruwa da na sama da harba makamai masu linzami a kewayen zirin Taiwan, da arewaci da kudanci da gabashin yankin na Taiwan. Atisayen mai lakabin "Joint Sword-2024B", wani mataki ne mai karfi na dakile ayyukan ‘yan aware dake neman ‘yancin kan Taiwan, kuma hakan mataki ne wajibi, halastacce na kare ikon mulkin kasa da dunkulewar sassanta.
Lai Ching-te, jagoran yankin Taiwan, wanda ke yunkurin neman ‘yancin kan Taiwan da kawo illa ga zaman lafiya, ya gabatar da jawabi a kwanan baya, inda ya kara nuna adawa da babban yankin kasar Sin da kara yin takala, kuma da gangan ya tada zaune tsaye tsakanin bangarori 2 na mashigin tekun Taiwan, lamarin da ya haifar da babbar illa ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin Taiwan. Babban yankin kasar Sin ta mayar da martani ne saboda Lai Ching-te ya yi takala ya yunkura neman ‘yancin kan Taiwan. Abin da babban yankin kasar Sin ya yi, mataki ne da ya wajiba kuma halastacce.
Rundunar PLA na gudanar da atisayen soja a zirin Taiwan domin hukunta wadanda suke yunkurin neman raba Taiwan daga kasar Sin, da kiyaye ikon mulkin kasa da cikakkun yankunan kasa, bisa doka, a maimakon yadda kasar Amurka ta ce, tana neman aron baki.
Batun Taiwan, yana gaba da kome cikin muhimman muradun kasar Sin. Rundunar PLA ba za ta dakatar da matakanta ba, illa masu neman ‘yancin kan Taiwan su daina yin takala. (Tasallah Yuan)