logo

HAUSA

Iran ta gargadi Amurka game da hadarin tura dakarunta Isra’ila domin lura da tsarin kakkabo makamai

2024-10-14 10:35:11 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Iran Seyyed Abbas Araghchi, ya gargadi kasar Amurka game da hadarin tura dakarun ta zuwa kasar Isra’ila, da nufin lura da na’urorin tsarin kakkabo makamai masu linzami ko THAAD.

Araghchi wanda ya bayyana hakan a jiya Lahadi cikin sakon da ya wallafa ta shafin yanar gizo, ya ce Amurka za ta jefa sojojin ta cikin hadari, idan har ta tura su Isra’ila domin lura da sarrafa na’urorin na THAAD kirar Amurka.

Ministan ya yi tsokacin ne a matsayin martani ga rahotanni dake cewa Amurka ta amince ta tura na’urorin na THAAD zuwa Isra’ila, matakin da ko shakka babu zai yi matukar jefa sojojin Amurkan cikin hadari. Ya ce Amurka na ci gaba da taimakawa Isra’ila da tarin tallafin ayyukan soji, wadanda ya zuwa shekarar nan ta 2024 ya kai dalar Amurka biliyan 17.9, adadin da ya kai matsayin koli a tarihi.

Daga nan sai mista Araghchi, ya bayyana matakan da Iran ke dauka a matsayin na kare barkewar rikicin kan iyakar yankunan kewayenta. Ya ce Iran ba ta da wani kaidi a fannin kare rayuka da moriyar jama’ar ta.

A ranar Juma’a hukumar tsaron Amurka Pentagon, ta tabbatar da cewa za ta aike da tsarin tsaron makamai masu linzami na THAAD zuwa Isra’ila, don taimakawa kasar kare duk wani farmaki na makamai masu linzami, biyowa bayan harin da Iran ta kaiwa kasar a kwanakin baya. (Saminu Alhassan)