Jirgin ruwa mai ba da aikin jinya na “Peace Ark ” na kasar Sin ya isa kasar Kamaru
2024-10-14 07:39:22 CGTN Hausa
A ran 7 ga watan Oktoba, jirgin ruwa na ba da jinya na rundunar sojin ruwan kasar Sin, wato jirgin ruwa na Peace Ark wanda ke aikin sada zumunta na shekarar 2024 a duk fadin duniya, ya isa tashar ruwa ta Douala ta kasar Kamaru domin fara ziyarar sada zumunta ta kwanaki 7 tare da gudanar da aikin jinya a wurin. Shi ne karo na farko da jirgin ya kai ziyara kasar Kamaru. (Sanusi Chen)