logo

HAUSA

Najeriya ta samu nasarar noma tan miliyan 9.2 na shinkafa a damunar bana

2024-10-13 16:26:29 CMG Hausa

Hukumar binciken al’amuran noma ta kasa tare da hadin gwiwa da ma’aikatar noma da bunkasa noman abinci ta tarayyar Najeriya sun fitar da rahoton dake nuna cewa, an samu noma adadin tan miliyan 9.2 na shinkafa yayin noman damunar 2024.

Shugaban hukumar Farfesa Emmanuel Ikani ne ya tabbatar da hakan ranar Jumma’ar 11 ga wata a birnin Abuja lokacin da yake gabatar da rahoto a kan mizanin rawar da Najeriya ta taka yayin noman damunar bana, ya ce adadin ya haura na damunar 2023 inda a wancan lokaci aka iya noma tan miliyan 8.1 na shinkafa.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

Farfesa Emmanuel Ikani ya ce an gudanar da wannan bincike ne a tsakanin ranakun 8 zuwa 15 ga watan jiya na Satumba, kuma binciken ya gudana ne bisa aikin hadin gwiwa da wasu hukumomi da aikinsu ke da nasaba da noma da bincike a game da irin shuka da kuma nau’ikan kwarika da suke addabar amfanin gona tun daga lokacin shuka har zuwa lokacin girbi.

Kamar dai yadda rahoton ya nuna cewa shugaban hukumar, jihar Niger na daya daga cikin jahohi 10 da suka noma shinkafa mai yawa a bana, inda jihar ta samar da tan dubu dari 7 sai jahohin Kogi da Benue da Kano da suke biye mata.

Haka kuma rahoton ya nuna cewa sama da filayen noma dubu 350 ne manoma suka gaza aikata su sabo da matsaloli na tsaro a Najeriya.

Daga karshe rahoton ya kawo shawarwari a kan yadda za a kara inganta harkokin noma a Najeriya, daga cikin su akwai shiri mai nisan zango da amfani da na’urorin zamani wajen aikin noma, samar da asusun amintattu da zai rinka bayar da taimakon gaggawa ga manoma, kara adadin yawan jarin da ake saka a fannin noma da rage yawan haraje-harajen da hukumomi ke karba a kan amfanin gona, da kuma dakatar da karbar kudade da jami’an tsaro ke yi a wajen direbobin da suke dakon kayan amfanin gona zuwa wasu sassan kasar. (Garba Abdullahi Bagwai)