logo

HAUSA

EIC: Masu zuba jari na kasar Sin na karfafa ci gaban tattalin arzikin Habasha

2024-10-13 16:40:57 Habasha Sin

Hukumar zuba jari ta kasar Habasha ko EIC ta ce, masu zuba jari na kasar Sin suna taka muhimmiyar rawa wajen karfafa ci gaban tattalin arzikin kasar Habasha, ta hanyar zuba jari mai dimbin yawa, da samar da ayyukan yi.

A cikin wata sanarwar da hukumar ta EIC ta fitar da yammacin ranar Juma’ar da ta gabata, ta bayyana cewa, a cikin shekarun da suka gabata wasu ayyuka 3,309 na kamfanonin Sin, sun zuba jari fiye da dalar Amurka biliyan 8.5 a kasar Habasha, lamarin da ya ba da gudummawa sosai ga manufofin tattalin arzikin kasar.

EIC ta kuma bayyana cewa, karuwar masu zuba jari na kasar Sin, ta fuskar yawan ayyuka da kuma kudaden dake shigowa, ta samar da kuzarin da ake bukata a tattalin arzikin Habasha.

Wadannan jarin sun samar da sama da 325,400 na guraben ayyukan yi na dindindin da na wucin gadi ga Habashawa a cikin 'yan shekarun nan, a cewar EIC. Bayan wata babbar ziyara da tawagar EIC ta kai yankin masana'antu na Gabas mai nisan kilomita 40 a kudu maso gabashin Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, hukumar ta bayyana cewa, sama da kamfanoni 150 ne ke aiki a yankin, inda masu zuba jari na kasar Sin suka kai sama da kashi 95 cikin dari na wadannan kamfanoni. 

Yankin masana'antu na Gabas, wanda masu zuba jari masu zaman kansu na kasar Sin suka gina, ana daukarsa a matsayin abin koyi ga raya yankin masana'antu na kasar Habasha, wanda hakan ya kara karfafa burin Habasha na zama cibiyar masana’antu na Afirka. (Yahaya)