logo

HAUSA

Najeriya ta bayyana damuwa bisa ci gaba da shigowar makamai cikin kasar daga Libya

2024-10-12 15:06:57 CMG Hausa

Hukumar binciken sirri a kan hada-hadar kudaden ta haramtattun hanyoyi a tsakanin kasa da kasa da kuma bibiyar yadda ake kashe kudaden gwamnati a Najeriya NFIU ta bayyana damuwa bisa yadda ake ci gaba da samun karuwar shigowar makamai cikin kasar daga Libya.

Shugabar hukumar Hajiya Hafsat Abubakar Bakari ce ta bayyana hakan a birnin Washington na kasar Amurka yayin wani taro da cibiyar bayar da shawarwari a kan harkokin mulki, ciniki da kuma tabbatar da adalci a hada-hadar kudade ta duniya ta shirya, ta ce ya zama tilas a tashi tsaye wajen lura da dillancin makamai a tsakanin kasa da kasa da kuma masu  safarar kudaden haram.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Kamar yadda yake kunshe cikin wata sanarwa dauke da sa hannun shugaban sashen sadarwa da hulda da jama’a na hukumar Sani Tukur wanda ya rabawa manema labarai jiya Juma’a 11 ga wata a birnin Abuja, hukumar ta NFIU ta alakanta karuwar ayyukan masu fasa kaurin makamai zuwa Najeriya bisa yadda ake ci gaba da samun matsalolin tashe-tashen hankula da hare-haren ’yan bindiga da ayyukan masu garkuwa da mutane a wasu sassan kasar.

Hajiya Hafsat Bakari ta ce, a sakamakon hakan ne hukumar ke kara jaddada kudurinta na ci gaba da daukar matakai domin yiwa tufkar hanci don rage kaifin tasirin irin wadannan dillalai ga harkokin tsaron Najeriya.

Ta shaidawa zauren taron irin nasarorin da Najeriya ke samu a yaki da safarar kudaden haram da kuma masu daukar nauyin ayyukan ta’addanci a kasar.

Ta ci gaba da cewa, hukumar tata tana samun dukkan goyon bayan da ya kamata wajen tafiyar da ayyukanta, amma dai duk da hakan tana matukar bukatar gudummawar kasashen duniya wajen nasarar yaki da ayyukan ta’addanci da kuma yaduwar kudaden haram a kasashen dake yankin Sahel da na tafkin Chadi. (Garba Abdullahi Bagwai)