logo

HAUSA

An kaddamar da ginin gidaje 882 ga dakarun tsaron Jamhuriyar Nijar

2024-10-12 16:11:45 CMG Hausa

A jiya Jumma’a ne ministan kula da harkokin cikin gida da tsaron al’umma na Jamhuriyar Nijar, Janar Mohamed Toumba, ya kaddamar da ginin gidaje 882, domin dakarun tsaron kasar a yankin yammacin wajen birnin Yamai.

Rahotanni sun ce bankin samar da muhalli na kasar ne ya samar da kudaden gudanar da aikin, wanda zai lashe kudi har sefa sama da biliyan 6.317, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 10.525. Kuma ana sa ran kammalar aikin nan da shekaru 3 masu zuwa.

Da yake jawabi yayin kaddamarwar, Toumba ya ce aikin zai zamo muhimmin mataki na sauya zamantakewar jami’an tsaro da iyalan su, inda za’a ba da fifiko ga jami’an da suka ji raunuka, yayin ayyukan yaki da ta’addanci da kasar ke fafutukar ganin bayan sa. (Saminu Alhassan)