Matsalar tsaro a yankin Sahel : Senegal ta bayyana goyon bayanta ga Burkina Faso
2024-10-12 18:46:37 CMG Hausa
Shugaban Burkina Faso, kaftin Ibrahim Traore ya gana, a ranar 10 zuwa 11 ga watan Oktoban shekarar 2024 a birnin Ouagadougou, tare da wata tawagar kasar Senegal a karkashin jagorancin manzon musamman na shugaban kasar Senegal Bassirou Diomaye Faye.
Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.
Shi dai, Abdoulaye Bathily, na dauke da sakon shugaba Bassirou Diomaye Faye zuwa ga takwaransa kaftin Ibrahim Tarore na Burkina Faso.
Na zo Burkina Faso tare da wata babbar tawaga, dauke da sakon shugaba Diomaye, in ji manzon musammun.
Wannan sako ya na kunshe da goyon baya na shugaba Diomaye Faye da gwamnatinsa da al’ummar kasar Senegal zuwa al’ummar kasar Burkina Faso cikin yanayin da ake ciki a yau da ke tattare da hare haren ta’addanci, in ji Abdoulaye Bathily.
Abdoulaye Bathily ya bayyana damuwar kasarsa gaban matsalolin tsaro da yankin Sahel ya ke fuskanta, da ma yammacin Afrika baki daya. Al’umominmu, yankinmu tun yau da jimawa suke bayyana fatan wani hadin kan ‘yan kasa, da ci gaba, da nasarori da kuma tsaro. Idan ana ganin abubuwan da ke faruwa a wannan shiyya a yau, dole hankali ya tashi.
Manzon musammun musamman na shugaba Faye, ya yi imani cewa wannan babi mai wahala ba za’a samu sa’ida ba sai da hadin gwiwa tsakanin al’umomi, da hadin kai da zumunci a tsakaninsu, inji mista Bathily.
Da ya ke magana game da kafa gamayyar kasashen yankin Sahel AES, da kuma muradun kasashe mambobi suke son cimma, manzon musamman na shugaba Faye ya bayyana cewa ko da yaushe idan wani gungun kasashe yi niyyar kafa hadaka domin cimma marudansu tare, abu ne mai kyau.
Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.