logo

HAUSA

Sin ta soki matakin Isra’ila na kaiwa wurin ajiyar kayayyakin tawagar MDD dake Lebanon hari

2024-10-11 20:29:52 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce Sin ta yi matukar Allah wadai da harin da sojojin Isra’ila suka kai kan ma’ajiyar kayayyaki ta tawagar MDD dake kasar Lebanon ko UNIFIL, lamarin da ya haifar da jikkatar jami’an wanzar da zaman lafiya na MDDr su 2.

Mao Ning, ta yi tsokacin ne a Jumma’ar nan, yayin taron zantawa da manema labarai da aka saba gudanarwa, inda ta ce duk wani hari kan jami’an wanzar da zaman lafiya, mummunan mataki ne na keta dokokin jin kai na kasa da kasa, da kuduri mai lamba 1701 na kwamitin tsaron MDD, kuma hakan ba abu ne da za a lamunta ba.

Jami’ar ta kara da cewa, Sin na bukatar a gudanar da bincike kan faruwar lamarin, da hukunta wadanda ke da hannu, da daukar matakan dakile sake aukuwar hakan. Kaza lika, ya wajaba dukkanin sassa masu ruwa da tsaki a rikicin su tabbatar da tsaron rayukan daukacin jami’an MDD, da kadarori ciki har da na dakarun UNIFIL.

Ta kara da cewa, Sin na kira ga daukacin sassan da batun ya shafa, musamman Isra’ila, da su gaggauta aiwatar da matakai na dakile kara tabarbarewar yanayin da ake ciki, da tabbatar da tsaron lafiyar dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD, da kandagarkin ci gaba da tabarbarewar rikicin, ko habakarsa zuwa matakin da zai gagara magancewa. (Saminu Alhassan)