MDD ta zartas da kudurin kafa yanayi maras shinge ga masu bukata ta musamman
2024-10-11 11:33:49 CMG Hausa
Jiya Alhamis, a taron majalisar hakkin bil Adama ta MDD karo na 57, an cimma matsaya daya wajen zartas da kudurin kafa yanayi maras shinge ga masu bukata ta musamman, ta yadda dukkan al’ummomin kasashen duniya za su kare hakkinsu yadda ya kamata. Wannan kudurin da kasar Sin ta gabatar a madadin kasashe guda 30 da suka hada da Kamaru da Honduras da Pakistan da kuma Turkiya da sauransu, shi ne kuduri na farko da MDD ya zartas ta fuskar kafa yanayi maras shinge ga masu bukata ta musamman.
Zaunannen wakilin kasar Sin dake ofishin Geneva na MDD, kana wakilin kungiyoyin kasa da kasa dake kasar Switzerland, Chen Xu, ya bayyana cewa, shirin kafuwar yanayi maras shinge ga masu bukata ta musamman ya nuna wayewar kan bil Adama, zai kuma ba da taimako ga dukkanin al’ummomin kasashen duniya da su cimma moriyar bunkasuwar zaman takewar al’umma cikin yanayin adalci, tare da cimma burin kiyaye hakkin bil Adama bisa dukkan fannoni.
A yayin taron, wakilai na kasashe da dama da suka hada da Cuba da Dominican da kuma Benin da sauransu sun ba da jawabai, inda suka furta cewa, kudurin ya ba da jagoranci ga ci gaban sana’a maras shinge, zai inganta bunkasuwar aikin kare hakkin bil Adama cikin kasa da kasa kamar yadda ake fata. Bayan da aka zartas da kudurin, jami’an ofishin hakkin dan Adam na MDD da wakilan kasashe da dama sun taya wakilan kasar Sin murna game da wannan batu. (Mai Fassara: Maryam Yang)