An bude babban taron kasa da kasa a kan sha’anin ilimi yara mata a Najeriya
2024-10-11 09:10:23 CMG Hausa
Mataimakin shugaban tarayyar Najeriya Sanata Kashim Shettima ya bukaci samun hadin kan dukkannin bangarori wajen shawo kan matsalolin nuna wariyar jinsi a fagen sha’anin samar da ingantaccen ilimi ga yara mata.
Ya bukaci hakan ne ranar Alhamis 10 ga wata a babban dakin taro na fadar shugaban kasa dake birnin Abuja yayin da ya jagoranci bude babban taron kasa da kasa kan harkar ilimin ’ya’ya mata. Ya ce, darajar ’ya mace a baiyane take a cikin kowacce wayayyar al`umma.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Mataimakin shugaban kasar ya ce, ya zama wajibi gwamnatoci a dukkannin matakai da sarakuna da kungiyoyin al’umma da kuma hukumomin ba da agaji na kasa da kasa su hada hannu wuri guda domin dai fito da wata manufa ta bai daya da za ta tabbatar da ganin cewa kowane yaro a Najeriya mace ko namiji ya sami ilimi ingantacce.
Sanata Kashim Shettima wanda ya sami wakilcin mataimakin shugaban ma’aikata a fadar shugaban tarayyar Najeriya Sanata Ibrahim Hadeja, ya ce, kowanne irin gyare-gyare a kan samar da manufofin ilimi na kasa gwamnati dai za ta yi cikakken amfani da shi domin samar da tabbataccen matsayi da zai baiwa yaran Najeriya damar yin karatu a cikin kowacce al’umma.
Ya ce, irin wadannan manufofi da za a samar dole ne ya kasance shugabannin al’umma tun daga matakin kauyuka da sarakuna da kuma malaman addini, suna da cikakkiyar masaniya a kai tare da fahimtar da su sosai a kan mummunan tasiri na rashin karatu ga makomar kasa, inda ya ce, babbar kadarar da za a baiwa ’ya’ya mata dai shi ne ilimi.
Mataimakin shugaban na tarayyar Najeriya ya ce, lokaci ya wuce da za a daina yin wasa da shigar ’ya’ya mata makarantu, a matsayinsu na iyaye, inda ya ce abin takaici irin wannan halayya ta fi a jihohin arewacin Najeriya. (Garba Abdullahi Bagwai)