logo

HAUSA

Kasar Sin a harba wani tauraron dan Adam zuwa can falakinsa dake sararin samaniya

2024-10-11 11:34:39 CGTN Hausa

Da misalin karfe 9 da minti 50 na daren 10 ga watan Oktoba, kasar Sin ta yi amfani da rokar dakon kaya samfurin B mai lamba 3 ta Long March ta harba wani tauraron dan Adam mai lamba 03 zuwa can falakinsa dake sararin samaniya kamar yadda aka tsara. Wannan tauraron dan Adam zai zama daya daga cikin taurarin dan Adam wadanda za su goyi bayan tsarin yanar gizo da kasar Sin ke ginawa a sararin samaniya mai nisa da duniyarmu. (Sanusi Chen)