logo

HAUSA

Shugaban Pakistan ya yi juyayin rasuwar Sinawa sakamakon harin ta’addanci

2024-10-11 14:29:06 CMG Hausa

Jiya Alhamis, shugaban kasar Pakistan Asif Ali Zardari ya je ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Pakistan, domin nuna juyayin rasuwar Sinawa da harin ta’addanci ya rutsa da su lokacin da ‘yan ta’adda suka kai hari kan jerin gwanon motocin kamfanin kasar Sin a tashar lantarki ta Qasim.

Shugaba Zardari ya bayyana cewa, a madadin al’ummomin kasar Pakistan, ya yi Allah wadai da wannan harin ta’addanci da kakkausan harshe, ya kuma nuna juyayi ga rasuwar wadannan mutane, tare da mika gaisuwar ta’aziyya ga iyalansu, ya ce, da fatan wadanda suka jikkata za su warke da sauri. Haka kuma, kasar Pakistan ta yi alkawarin daukar matakai yadda ya kamata domin kama wadanda suka aikata wannan laifi, da kuma kare tsaron Sinawa dake zaune a kasar Pakistan. Kana, za ta karfafa aikin yaki da ta’addanci a dukkan fannoni, ba za ta lamunci duk wani matakin da zai bata zumuncin dake tsakanin kasashen biyu, ko illata hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu wajen shimfida zaman lafiya da neman ci gaba tare ba.

Bayanin da ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta fidda ya nuna cewa, bayan aukuwar harin, kasar Sin ta tura tawagar aiki zuwa kasar Pakistan nan take domin gudanar da aikin gaggawa tare da ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Pakistan, da kuma kamfanonin da abin ya shafa. Tawagar ta riga ta gana da jami’ai na ma’aikatar harkokin wajen kasar Pakistan da na rundunar ‘yan sanda da kuma wakilai daga hukumar leken asiri na kasar, inda ta bukaci bangaren kasar Pakistan da su aiwatar da harkokin bayan harin kamar yadda ake bukata, su kuma dukufa wajen ba da jinya ga wadanda suka jikkata, da gudanar da bincike daga dukkan fannoni domin gano gaskiyar batun, tare da hukunta wadanda suka kai wa motocin kamfanin kasar Sin hari. Haka zalika kuma, tawagar ta yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su dauki matakai yadda ya kamata wajen kare zaman lafiyar Sinawa da tsaron hukumomi da ayyukan kasar Sin dake kasar Pakistan. (Mai Fassara: Maryam Yang)