logo

HAUSA

Yawan kudin shiga na sha’anin yanar gizo a kasar Sin daga watan Janairu zuwa Agustan bana ya karu da kashi 4.4%

2024-10-10 11:06:38 CMG Hausa

 

Bisa kididdigar da hukumar masana’antu da sadarwa ta kasar Sin ta bayar, an ce, daga watan Janairu zuwa Agustan bana, kudin shiga na sha’anin yanar gizo a kasar ya samu bunkasuwa mai dorewa, inda aka samu karuwar kudin nazari.

Alkaluma sun nuna cewa, a cikin wadannan watanni 8, yawan kudin da kamfanoni masu ruwa da tsaki masu matsakaicin girma suka samu ya kai kimanin dala biliyan 166, adadin da ya karu da kashi 4.4% bisa na makamancin lokacin bara. Yawan kudin da kamfanonin yanar gizo masu matsakaicin girma suka zuba kan nazari ya kai kimanin dalar biliyan 8.8, wanda ya karu da kashi 7.5% bisa na makamancin loakcin bara.

Kaza lika, yawan kudin shiga da kamfanoni masu ba da hidima a bangaren sadarwa suka samu a wadannan lokuta ya karu da kashi 7.5% bisa na makamancin lokacin bara, yayin da kudin shiga da kamfanoni masu ba da hidimomi ga zaman rayuwar yau da kullum a bangaren yanar gizo ya karu da kashi 3.8%. (Amina Xu)