logo

HAUSA

Firaministan Sin ya yi kira da a karfafa dunkulewar nahiyar Asiya

2024-10-10 20:42:49 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya yi kira ga bukatar karfafa kasancewar nahiyar Asiya tsintsiya madaurinki daya, yana mai cewa, kasashen Asiya na da muhalli da muradu da damarmaki da akidu na bai daya.

Li Qiang ya bayyana haka ne yau Alhamis, yayin jawabinsa ga taro karo na 27 na kasashen ASEAN da wasu kasashe 3 a birnin Vientiane na kasar Laos, inda ya ce kasashen Asiya na girmama ’yancin kai, yana mai cewa, ya kamata a tafiyar da harkokin nahiyar ta hanyar tuntubar al’ummarta, kana ya kamata makomar nahiyar ta kasance a hannunta.

Firaministan ya kara da cewa, dukkan kasashen Asiya sun jaddada cewa, ci gaba shi ne abun dake gaba da komai, kuma sun amince cewa, zaman lafiya na da matukar muhimmanci. (Fa’iza Mustapha)